Shin akwai Sardauna a Arewa?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Kowanne yanki ka iya samun wani jan gwarzo da kan sadaukar da kan sa don bunƙasa yankin. Akasarin irin waɗannan gwarazan ka iya tsintar kan su a gidan yari ko ma a yi mu su kisan gilla. Sauƙin lamarin shi ne aiyukan alherin irin wadannan mutane kan wanzu shekaru aru-aru bayan rayuwar su. Idan mutum ya shuka alheri to ba shakka alherin zai bi shi har ma ya iya amfanar zuriyar sa su zama masu albarka. Hausawa kan ce alheri gadon barci. Mu duba rayuwar Shehu Usmanu Mujaddadi wanda dududu shekara 63 ya yi a duniya amma har yau bayan fiye da ƙarni biyu da rasuwar sa a na cin gajiyar aiyukan sa. Mujaddadi ya yi nasarar kafa babbar Daula mai bin tsarin addinin Musulunci tsanta da kore dukkan tsafe-tsafe da tsubbace-tsubbace da kafircewa dokokin Allah. Turawan mulkin mallaka sun zo yankin da yau ya ke zaman Nijeriya su ka yaki Daular ta Shehu da kasha mutane da dama ciki kuwa har da Sultan ɗin Daular na ƙarshe Sultan Attahiru inda su ka kafa sarauta kadai ba tare da amfani da Musulunci tsantsa ba. Karshe ma sun yi nasarar mayar da masarautun da su ka wargaza zuwa na kare al’adu ko gargajiya. Duk yanda Sarki ke son bin tsari irin na musulunci ba zai iya ba don yanzu ya na amsa kujerar sarautar gargajiya ne. Abun fahimta a nan Daular Shehu ta zama tarihi tun shigowar turawa wannan yanki da ya hada da arewacin Nijeriya. Don mutum ya ga Sarki a wannan zamani ya zarme ko ya rungumi gargajiya to dama wannan Sarkin na zamanin turawan mulkin mallaka ne. Za a kara fahimtata in na ce sarakunan kan iya zama jikokin marigaya da su ka yi jagoranci a Daular da Shehu ya kafa amma ba lallai ne su na iya kamanta wancan mulkin ba don wa imam tarnakin tsarin mulki da ya maida sarakunan na gargajiya ko kuma wajen zabar sarakunan ma sai an duba wanda bokon saya bokance tukun kafin a naɗa shi. Mu lura duk da turawa sun ruguza Daular Shehu sai Allah ya yi wa zuriyar sa albarka da samun wasu haziƙai da su ka shuka alheri musamman wajen raya Lardin Arewa don amfanin dukkan mazauna yankin kama daga Musulmi, mabiya addinin Kirista, ‘yan gargajiya da ma kowa don bin adalci. Tauraron da ya baiyana sosai shi ne Firimiya Sir Ahmadu Bello Saradunan Sokoto Gamji mazan kwarai wanda a ranar 15 ga watan Janairu 1966 miyagun iri maƙiya Arewa su ka kulla makirci wajen yi ma sa kisan gilla. Bawan Allah bai tara dukiya ba don babban matsayin da ya rike.

Taƙarƙarewa da waɗanda su ka karɓo kwangilar wargaza arewa su ka yi na cin zarafin Shehu Usmanu Mujaddadi ba abun mamaki ba ne in an kula da irin aikin alherin da ya shuka da ba yanda za a yi ka kawo tarihin wannan yankin na arewa har ma da kan iyakokin ƙasashen da ke makwabtaka ba ka ambaci ayyukan kafa ilimi da kawar da miyagun al’adu da Shehu ya yi ba. Haƙiƙa Mujaddadi ya bunkasa neman ilimi da bautawa Allah madaukakin Sarki bisa koyarwar Manzon Allah mai tsira da aminci. Masu jin haushin ayyukan Shehu na hana batsa da fitsara, tsafe-tsafe, ‘yan bori da shakiyanci don cin bulus a duniya lahira ko oho sun ɓullo a wannan zamanin ta hanyar jikokin su da ba su tuba ba. Ai wanda ba ya son sallah ko kuma ya na so a bar shi da sunan Musulmi amma sai ya ga dama ya yi sallah ko azumi; ba zai so Shehu ba. Jikokin matsiyatan zamanin Mujaddadi sun ɗau matakin cusa ƙarairayi a tarihin Shehu da kagen wai ya yaƙi musulmi, sam-sam Shehu ba inda ya yaki musulmi, hasalima ma Sarkin Gobir Yunfa wanda ba Musulmi ba ne, shi ya kai farmaki kan Shehu don kashe shi kowa ma mai kin jinin Musulunci ya sarara da kuba barasar sa.

Zuwan Mujaddadi babban alheri ne ga yankin arewa da kewaye don tabbas in da turawan mulkin mallaka sun shigo sun samu yankin kara zube gabanin hasken Shehu, yau da wani labarin wani addini a ke yi daban na shirka, tsafe-tsafe da shirme.

In ka na son gane alherin mutum ko ɗabi’ar sa to ka kalli abokan sa za ka fahimci lamura da yawa. In kuma rai ya yi halin sa duba tarihin sa da yadda zuriyar sa ke rayuwa za ka fahimci alheri ko akasin haka da ya shuka. Cikin jikokin Shehu Mujaddadi akwai uban al’ummar arewa kakaf ko mutum ya na so ko ba ya so; namiji uban ‘yan boko “Amadun Amadu mai tawakkali gun Allah jikan mai saje…mai dubun nasara garnakaki Sardauna…ya gyara masallacin Bello da masallacin Shehu” A waƙar marigayi dakaren mawaka Alhaji Musa ɗankwairo Maradun. “Tun a da a can zamanin zamuna, tun a zamanin Shehu bi Fodiyo, Shehu ya tattara almajirai ne ya ce zuriya ta wa ’yan can na baya, su za su kira yi ni inda ban kira ba, a yau ga shi mun gan ta gun Aamadu” A wakar Sarduna kakan ka bi Hodiyo ta jagoran mawakan Hausa na duniya rankatakaf Mahdi mai dogon zamani Dokta Alhaji Mamman Shata Katsina na Sarkin Daura Alhaji Mamman Bashar Dan Musa.

Sardauna Ahmadu wanda a ka haifa a Rabah jihar Sakkwato ta yau a 1912 dan hakimin Rabah ne Ibrahim Bello Atiku, shi kuma dan Atiku ne jikan Sultan Muhammad Bello ne wanda dan Shehu Mujaddadi ne Danfodiyo. A fili ya ke Ahamdu Bello ya ɗauko ɗabi’ar haƙuri da jajircewa ta Mujaddadi inda ya riƙe dukkan al’ummar arewa ba tare da nuna bambancin wariyar addini ko ƙabila ba. Mu koma tarihin marigayi Sarkin Kagoro, Micheal Audu Buba, Su Chief Sunday Awoniyi kai har ma ga Nzegwu Kaduna dan ƙabilar Ibo wanda ya yi wa Sarduna kisan gilla. Duk wadannan mutanen sun zauna da Sardauna kuma sun san ɗabi’un sa na son jama’a da kare haƙƙin marar sa ƙarfi.

Ko ban ce a rubuta a ajiye ba, kwanan nan ‘yan kwangilar rusa arewa za su dawo kan Sardauna da kazafi da cin mutunci don aiyukan alherin sa da su ka haɗa da sauko da wasu daga kakannin su daga kan tsaunuka suna sanya ganye a matsayin sutura ya tufatar da su ya dawo da su hanyar kwarai kamar yadda ya gada daga Mujaddadi.

Matasa na zamanin yau su shirya tafiya babbar cibiyar Arewa wato Kaduna don ziyartar Arewa House inda a ka kashe Sarduna kuma nan ne ke ƙunshe da wasu kaya na tarihin sa. Hakika Sardauna bai tara dukiya ba amma ya tara ɗimbin daraja da sadaukar da kai don ƙarfafa arewa a wani shirin sa mai taken “northernization policy” wanda ya jawo ma sa bakin jini daga magabtan arewa su ka shirya don majusanci su ka sa bindiga su ka harbe Amadu! Jinin ka Sardauna bai tafi a haka kawai ba don ka shuka alheri da nagartattun ‘yan arewa har ma da sakarkarun ke cin gajiya har karshen rayuwa.

KAMMALAWA

GIMBIYA GARDI NE – Ga misalin ɗaya daga shafukan yanar gizo da ke rura wutar fitina tsakanin manyan ƙabilun Arewa. Ina son ‘yan uwa a gane “Gimbiyar Hausa” ba wata mata ba ce ta buɗe shafi don ƙaryar kishin Hausawa, a’a wani gardine ya buɗe da ba da dama ga kananan ‘yan kwangilar rusa Arewa a matsayin “admins” akwai ma “screenshot” na yaron gardin da ya haska ba mace ce Gimbiya ba. Wasu kan rudu da haka har su na rubuta “ba a bin ki bashin hujja..” a sharrin da gardin ke yaɗawa. Na ba shi shawara ya canja suna zuwa GIMBIYI ba GIMBIYA ba don ya fito a gardi a san shi. A gefe guda “Jarumar Hausa” mace ce Bamagujiya wato Kaltume Alimbe Jitami. Illar da ta ke yi ba ta kai ta gardin nan ba don ita tuni ta fito fili da dirar mikiya kan magabatan kwarai. Gardin nan kan yanko rubutun Larabci don yaudarar mutane alhali ko a jikin kwalin sigari a kan iya rubuta Larabci. Gardi kan kifar da ma’anonin bayanan litattafan magabata don kunna fitina. Mutanen kan yi saurin yarda in sun ga rubutun Larabci. “Chatgpt” na fasahar AI na taimakawa jahilan nan wajen kwangilar. Wallahi in da za su fito fili a gwabza da su sai asirin su ya tonu. Hausar kan ta ba su iya ba don bakin su ko harshen su ya kasa lankwashewa ya iya furta kalmomin Hausa tsab. Na ji wani ma a cikin su ya yi karambanin jan wani hadisi inda hadisin ya ke jan sa kamar hanjin barira. Insha Allah zan fito da hoton GIMBIYI don a gane shi. GIMBIYI ba Bahushe ba ne sam-sam. Hatta kunnen sa ya yi kama da zanen Dujal.

Haƙiƙa tun da annamiman nan su ka aibanta Shehu Mujaddadi su ka diro kan uban Arewa kakaf Sir Ahmadu Bello Sardauna, nan gaba kuma za su sauka kan manyan malaman musulunci ne da su ka kare rayuwar su wajen wa’azi da faɗakarwa ga al’ummar arewa. Ba za su saurarawa malami daga kowace fahimta ya fito ba matuƙar aibanta shi da za su yi zai dace da kwangilar da a ka ba su ta hada Musulmin Arewa yaƙi da juna da fakewa da ƙabilanci. Na hango cin mutuncin magabata zai fara daga kan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi zuwa kan dattijo da ke raye Sheikh Dahiru Usman Bauchi musamman don shi Bafulatani ne. Ba inda Musulunci ya koyar da aukawa ƙabilanci. Da Bahuase da Bafulatani duk abu ɗaya a inuwar musulunci. Ya zama mai muhimmanci Hausawa da Fulani da ma sauran ƙabilun Arewa su farka don yaƙar wannan fitina da ke tinkarowa. Ba ma musulmi ba hatta mabiya addinin Kirista da waɗanda ma ba ruwan su da kowane addini har ma da masu bin addinin gargajiya, su sani in wannan fitnar ta iso to ba wanda zai tsira. Lallai mai gidan gilashi ya guji wasan jifa.

By ukarofi