Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya rantsar da sabbin masu bashi shawara guda biyu.
Sun haɗa da Hon. Tasi’u Dahiru Ɗanɗagoro a matsayin mai baiwa gwamna shawara akan Ilimin Alkur’ani da yaran da ba su zuwa makaranta.
Sai Hon. Aminu Lawal Jibia wanda aka rantsar a matsayin mai bai wa gwamna shawara akan inganta rayuwar al’umma.
Aminu Lawal ya taɓa riƙe muƙamin shugaban karamar hukumar Jibiya,ya kuma riƙe muƙamin mai ba gwamna shawara a gwamnatin Aminu Bello Masari kafin ya sami wannan muƙami.
Haka shima Hon Tasi’u Dandagoro ya taɓa riƙe muƙamin shugaban karamar hukumar Ɓatagarawa har karo na biyu,daga baya ya riƙe muƙamin kwamishinan ayyuka a gwamnatin Masari kamin samun wannan muƙami.
A jawabinsa bayan da ya jagoranci rantsuwar, gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana sabbin masu bashi shawara a matsayin ƙwararru da suka riƙe muƙamai daban daban inda suka nuna gaskiya da riƙon amana.
A cewar Gwamnan bai zaɓen tumun dare ba domin “Ina da tabbacin za su ba mara ɗa kunya.
Da ya juya kan muƙamin Hon Dandagoro ya ce , gwamna ya bayyana rawar da ilimin Kur’ani ke takawa da ya ce akwai buƙatar a magance ƙalubale da yaran da basa zuwa makaranta suke fuskanta.
“Ina mai tabbacin Tasi’u Dandagoro na da ƙwarewa da jajircewar da zai kawo ƙarshen waɗannan matsaloli,”Inji Dikko Raɗɗa.
A kan Aminu Lawal Jibiya kuwa, gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana shi a matsayin mutumin mutane a cikin al’ummarsa wanda hakan zai bashi damar aiwatar da tsare-tsaren gwamnati na cigaban al’umma.
Bikin rantsuwar da ya wakana a ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar ya sami halartar mayan jami’an gwamnati da yan’uwa da abokan arziki.
