Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalissar Agaji ta ƙungiyar JIBWIS ta Katsina ta naɗa Alhaji Garba Galadima Charanchi a matsayin sabon Daraktan agaji na ƙungiyar.
Ƙungiyar ta gabatar da sabon Daraktan Agaji na ƙungiyar ga shugaban ƙungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatul sunnah reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan Sauttus sunnah.
Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya yi maraba da tawagar tare da yaba musu bisa jajircewa wajen tallafa wa al’umma ta fuskokin agaji da jin ƙai.
Ya kuma buƙaci sabon daraktan da sauran mambobin majalisar da su mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu cikin gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa al’umma na amfana da wannan hidima ta addini da alheri.
“Wannan mataki na Majalisar Agaji ya nuna yadda ƙungiyar JIBWIS a Jihar Katsina ke ci gaba da haɓaka ayyukan jin-ƙai da samar da tallafi domin taimakon jama’a, musamman marasa galihu,”inji Sauttus sunnah.
Naɗin sa ya biyo bayan rasuwar tsohon daraktan ƙungiyar malam Abdullahi Na Bakori.
