2025: An fito da ƙa’idojin gasar gajerun labarai ta Ranar Marubuta Hausa ta Duniya

Spread the love

Daga BILKISU YUSUF ALI

Kwamitin gudanarwa da tsare-tsare na shirya taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya fitar da ƙa’idojin shiga gasar gajerun labarai na taron, wanda za a gudanar a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa a wannan shekara ta 2025.
Dr. Mujaheed Abdullahi Kudan ne ya sanar da ƙa’idojin a madadin kwamitin gasar a wata sanarwa cikin makon nan, inda ya bayyana cewa, “daga cikin tsare-tsaren bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya na shekarar 2025, wanda za a gabatar a Dutse na Jihar Jigawa a ranakun 31/12/2025 zuwa 01/01/2026. An shirya gasar rubutun gajerun labaran Hausa a kan batun fasahar AI da tsaro domin ta dace da taken taron na bana, wato Marubuta a ƙarni na 21: Ƙalubalen Tsaro da Tattalin Arziki. Gasa ce wadda za ta kasance a buɗe ga dukkan masu sha’awar shiga daga marubuta maza da mata sanannu da sababbi da ma masu sha’awar fara rubutu matuƙar za su kiyaye ƙa’idojin gasar.”
Sanarwar ta yi ƙarin kamar haka;
Maudu’in gasar:
Gudunmuwar fasahar AI ga tsaro da tattalin arziki
Manufofin gasar:

  1. Ƙarfafa marubuta su yi nazari kan yadda fasahar AI (Artificial Intelligence) ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziki.
  2. Samar da sababbin ra’ayoyi da mafita na zamani da za su iya taimaka wa al’umma wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki.
  3. Gina wata hanya ta tattaunawa da musayar ra’ayi kan amfanin fasahar zamani a cigaban ƙasa.
  4. Ba wa marubuta damar nuna fasaha da basira da ƙwarewarsu a fannin rubutu da bincike ko ƙirƙira.
  5. Haɗa marubuta da masu amfani da fasahar zamani domin a samu haɗin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki.
  6. Ƙarin samar da abin karatu mai inganci da manufa cikin harshen Hausa.
    Tsare-tsaren shiga gasar:
  7. Za a aiko da samfurin labarin da za a rubuta cikin kalmomin da ba su gaza 500 ba kuma ba su wuce 800 ba, ta wannan adireshin; [email protected] daga ranar 21/09/2025 zuwa ranar 21/10/2024.
  8. Za a tace a zabi 30 cikin samfurin labaran da aka turo waɗanda suka fi burgewa a cikin kwanaki goma (21/10/2025 zuwa 31/10/2025).
  9. Za a yi bita ta musamman ga masu waɗannan samfurin labaran 20 a kan fasahar AI da tsaro da tattalin arziki da kuma rubutun gajerun labarai(musamman saboda sababbin marubuta).
  10. Bayan bitar, za a buƙaci kowannensu ya rubuto cikakken labarinsa wanda bai gaza kalmomi 1000 ba kuma bai wuce kalmomi 1,500 ba bayan bitar, daga 15/11/2025 zuwa 15/12/2025.
  11. Za a bayyana labaran da suka yi nasara a wajen bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya 2025.
    Sharuɗɗan shiga gasar:
  12. A tabbatar rubutun ya dace da batutuwan da suka shafi fasahar AI musamman dangane da tsaro da tattalin arziki.
  13. A tabbatar an yi amfani da daidaitacciyar Hausa kuma an kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa. Dole ne amfani da haruffa masu lanƙwasa(ɓ, ɗ, ƙ, ‘y).
  14. A tabbatar an aiko da rubutun a tsarin Microsoft word ko PDF zuwa ga wannan email ɗin; [email protected]. tare da shedar yin rijista.
  15. A tabbatar ba a taɓa shiga wata gasa da labarin da za a turo ba, kuma ba a taɓa bugawa a jarida ko wata kafa ko zaurukan kafafen sadarwa na zamani ba.
  16. Wanda yayi rijista da taron ranar marubuta Hausa ne kaɗai zai iya shiga gasar.
  17. Mutane biyu za su iya shiga gasar da labari ɗaya. Kuma dole ne a aiko da labari cikin lokacin da aka ƙayyade.
  18. Kada labarin ya zamto ya ci zarafi ko tozarta wata al’umma ko ɗaiɗaikun mutane.
  19. Ba a yarda a sake ɗaukar duk labarin da aka shiga da shi gasar a sake shiga wata gasar da shi ba.
  20. A sani, hukunci da sakamakon alƙalan gasar shi ne na ƙarshe, ba za a sake tattauna shi ba a wani waje.
  21. Kowane marubuci na iya shiga gasar ban da mambobin kwamitin ƙoli na shirya wannan taro.
    Kyaututtukan da gasar za ta samar:
  22. Za a bayar da kyaututtuka ga labarai uku da suka yi zarra a matakin na ɗaya zuwa na uku.
  23. Za a bayar da takardar shaidar karramawa da awalajar litattafai ga waɗanda suka shiga gasar daga na ɗaya zuwa na 15 kuma za a duba yiwuwar buga labaran nasu cikin littafin da za a ƙaddamar da shi a taron shekara mai zuwa ta 2026.
    Mujaheed Abdullahi Kudan, Ph.D.
    A madadin Kwamitin Shirya gasar Ranar Marubutan Hausa 2025.

By ukarofi