Da Ɗumi-Ɗumi: An naɗa Sheikh Saleh bin Humaid a matsayin sabon babban mai fatawa na Saudiyya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Masarautar Saudiyya ta naɗa Sheikh Dakta Saleh bin Humaid a matsayin sabon mai fatawa na ƙasar kuma shugaban babbar majalisar manyan malamai.

Sarki Salman ya naɗa Sheikh Humaid a muƙamin kwana ɗaya da rasuwar Sheikh Abdulaziz bin Abdullah al-Sheik, kamar yadda jaridar Inside the Harmain ta wallafa a yau Laraba.

A jiya Talata Sheikh Abdullah al-sheik ya rasu yana da sama da shekaru 80 a duniya bayan shafe sama da shekaru 25 a muƙamin.

A shekarar 1949 aka haifi Sheikh Humaid, wanda ɗaya ne daga cikin limamai tara na babban masallacin Makkah. Haka kuma mamba ne shi a Majalisar Saudiyya tun daga 1993 kuma ya riƙe muƙamin kakaki na Majalisar Shura daga Fabarairun 2002 zuwa Fabarairun 2009.

A baya ya yi aiki a matsayin shugaban harkokin addini na masallatai masu alfarma biyu daga 2001 zuwa 20032

By Babaji