Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Musiba ta auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u da Aina’u Nuhu.
Sai dai mijinta, wanda shi ma ya samu rauni a sakamakon faruwar lamarin, tuni an sallamo shi bayan duba lafiyarsa a asibiti.
Wani maƙwabcinsu, Malam Ahmed, ya shaida wa Manhaja cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asubahi, lokacin da iyalin ke barci.
Sai dai ya ce “a gaskiya wannan tsohon gini ne da aka bari babu gyara, wanda hakan ne ya sa ya rushe.
“Ba zato ba tsammani kawai ginin ya faɗa musu,” inji shi.
Tuni dai an yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
