ADC ta zargi Gwamna Nasir da takardun karatu na bogi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen jihar Kebbi ta zargi gwamnan jihar Malam Nasir Idris da amfani da takardun bogi da ya ce ya yi karatu a waɗansu makarantu da ana tunanin ba gaskiya ba ne.

Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Engr Abubakar Atiku Musa sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar jiya Alhamis 28 ga Agusta, 2025.

Takardar ta bayyana jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen Jihar Kebbi, ta lura da damuwa game da rashin tabbas da ke tattare da bayanan karatun Gwamna Nasir Idris kamar yadda aka bayyana su a shafin Wikipedia.

Takardar ta ƙara da cewa ana nuna cewa Gwamna Idris yana da waɗannan takardun shaidar kammala karatu da suka haɗa da digirin MBA daga Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato, digirin digirgir (Ph.D) a fannin Ilimi daga wata jami’a da ba a bayyana ba.

“A matsayinmu na jam’iyya mai kishin gaskiya da riƙon amana, ADC na ganin cewa idan ba a fayyace wannan lamari ba, hakan zai iya jefa shakku ga amincin shafin Wikipedia da kuma mutuncin Gwamna Nasir Idris a matsayin jagoran Jihar Kebbi.

“Saboda haka jam’iyyar adawa ta ADC reshen Jihar Kebbi ta yi kira ga gwamna Nasir Idris da ya gaggauta bayyana cikakken bayani kan takardun karatunsa, ciki har da sunan jami’o’in da suka ba shi da shekarun da aka ba shi takardun, da kuma takardun shaida na hukuma.

“Masu gyara da kula da shafin Wikipedia, da su duba wannan bayanin da ke kan shafin gwamnan, su tabbatar da sahihancinsa tare da gyara inda ya dace, kamar yadda ƙa’idar Wikipedia ta tanada.”

Jama’ar Jihar Kebbi na da hakkin sanin gaskiya daga shugabanninsu. Takardun karatu ba sirri ba ne kawai, suna da matuƙar muhimmanci wajen gina amincewa da cancantar shugaba, musamman wanda ke riƙe da babban muƙami irin na Gwamna.

Don amfanin gaskiya, ingantaccen mulki, da tabbatar da adalci, jam’iyyar ADC reshen Jihar Kebbi tana neman a fitar da bayani kai tsaye wanda ke bayyana Gwamna Nasir Idris yana da MBA da Ph.D na gaskiya.

By ukarofi