Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Talata ne rundunar sojin ruwan Nijeriya a Badagry a Legas, ta mika buhunan tabar wiwi guda takwas da kudinsu ya kai Naira miliyan 12.8 ga hukumar yaqi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA a Badagry.
Laftanar Adedeji Adeyemi, Kwamandan Tsaro na cikin gida mai wakiltar bataliyar FOB, Commodore Aiwuyor Adams-Aliu, ya ce jami’an sojin ruwa sun kama abinda ake zargin tabar wiwi ne a ranar Litinin a unguwar Abojedo da ke kusa da gavar tekun Sultan, a Badagry.
A cewar Mista Adeyemi, bataliyar ta FOB, ta yi aiki ne a kan bayanan sirri kan ayyukan fasakwauri da ake zarginsu da aikatawa a yankin da take gudanar da ayyukanta.
“Bayanan sun nuna cewa an ga mutanen da suke saye da sayar da kayayyakin da ake zargin tabar wiwi ne a unguwar Abojedo, dake gabar tekun yankin FOB.
“Saboda haka, bataliyar Base Quick Response Team, ta tafi wurin da ake aikata laifukan domin gudanar da bincike tare da yin kame.
“Rundunar ta gudanar da aikin sintiri da bincike a yankin kuma ta kwato jimillar buhu takwas na kayayyakin da ake zargin sun kai Naira miliyan 12.8.
“Wadanda ake zargin ‘yan fasa-kwaurin sun gudu bayan da suka ga tawagarmu ta ‘yan sintiri yayin da aka kuma bincika al’ummomin da ke makwabtaka da su amma ba a samu wasu kayayyaki ko wadanda ake zargi ba,” inji shi.
