Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin yi wa ma’aikata karin albashi ta hanyar sake tsarin mafi kankantar albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.
Gwamnatin Tarayya za ta yi hakan ne bisa yin la’akari da tsadar rayuwar da ake fuskanta a fadin kasar nan.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka a ranar Litinin, a cikin jawabin murnar shiga sabuwar shekarar 2024.
Ya ce za a qara albashin ne domin kowane dan Nijeriya ya ji a jikinsa cewa gwamnati ta na kula da halin da ya ke ciki, musamman marasa galihu, talakawa da fakirai da matsakaitan karfin tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.
Farkon watan Disamba ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara biyan sabon tsarin albashi daga Afrilu 2024.
Ministan Yaxa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne a lokacin ya ce Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta fara biyan ma’aikata da sabon tsarin karin albashi daga ran 1 ga Afrilu, 2024.
Ministan Yada da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ya bayyana haka a ranar Alhamis, a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
Idris ya ce gwamnatin tarayya za ta daina biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi daga karshen watan 2024.
Bayan wani nazari mai zurfi da majibinta kula da harkokin kudaden gwamnatin tarayya suka yi, an bayyana cewa Gwamnatin Tarayya din za ta kashe har naira tiriliyan 24.66 a shekarun 2024, 2025 da 2026 wajen biyan albashi.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur a ran 29 ga Mayu, 2023, sai Gwamnatin Tarayya ta bijiro da karin naira 35,000 kan gundarin albashin kowane ma’aikacin, a matsayin tallafin rage radadin tsadar rayuwa na wani takaitaccen lokacin watanni shida.
To sai dai kuma a lokacin, kungiyar kwadago ta tayar da kayar baya cewa tallafin na toliyar naira 35,000 kan albashin ma’aikata, lasa zuma a baki ne, tunda ba na dindindin ba ne.
Maimakon haka, ‘yan kwadago sun karci kasa tare da jajircewa lallai sai dai a yi karin albashi dungurugum a 2024.
Bayan shafe watanni ana je-ka-ka-dawon tattaunawa, wakilan Gwamnatin Tarayya ta da na Majalisar Tarayya Al’amurran Ma’aikatan Tarayya (NPCNC), sun cimma amincewa dangane da batun naira 30,000 mafi kankantar albashi daga ran 18 ga Oktoba, 2019.
Sai dai kuma a ranar Alhamis kungiyoyin kwadago sun bayyana cewa sun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, tare da jaddada cewa dokar biyan hakkin leburan Gwamnatin Tarayya ta shar’anta cewa duk bayan shekaru biyar a rika yi wa ma’aikata karin albashi.
