Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da masu hannu da shuni wajen tallafa wa ilimi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen hadin gwiwa da masu hannu da shuni wajen daukar nauyin harkar ilimi a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karvi bakuncin shugabannin gidajen yada labarai a ofishinsa a ranar Talata a Kano.

Ya ce matakin na daga cikin matakan bunkasa fannin ilimi, wanda tun daga hawan gwamnatinsa, ta sanya dokar tabaci.

Ya kara da cewa, “ba za mu iya tallafa wa ilimi mu kadai ba sai da taimakon masu hannu da shuni, don haka akwai bukatar mu hada hannu da su don cimma nasarar aikin da ke gabanmu.

“Wannan wata hovvasa ce ta kokarin tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki sun bada gudummuwarsu wajen gyara fannin.”

A cewarsa, an dauki matakin ne da nufin samar da ingantaccen tushe ga ilimi, musamman a matakin farko da na sakandare domin tabbatar da ingantaccen aiki.

“Za mu gayyaci masu hannu da kamfanoni, abokan ayyukan ci gaba da hukumomin ba da agaji ta wannan hanyar,” inji shi.