Ba abin da ya fi a rayuwar mace kamar ɗora ta kan hanyar ilimi – Mariya Durumin Iya

“Mace na rayuwa ne ƙarƙashin kulawar wasu har ƙarshen rayuwarta”

Ci gaba daga makon jiya

Daga AISHA ASAS

A satin da ya gabata, mun fara shimfida kan tattaunawar da muke yi da daya daga cikin matan Arewa da suke da gidauniyar taimakon al’umma, inda muka soma da jin tarihin rayuwarta, yadda ta fara tunanin bude wannan gidauniyar da kuma hanyoyin da ta bi har hakarta ta cimma ruwa.

A wannan sati, za mu soma ne da samar wa masu karatu amsar tambayar da muka kwana kanta, kamar yadda muka yi alkawari, kafi wasu tambayoyin su biyo baya.

Har wa yau dai, Aisha Asas ce tare da Mariya Inuwa Durumin Iya.

MANHAJA: Menene ayyukan wannan gidauniyar?

MARIYA DURUMIN IYA: Gidauniyar na da ayyuka masu yawa, masu fadi, duk da dai mun takaita su, to amma manya-manyan ayyukanmu akwai kula da iyayen marayu. Mu kan taimaka masu da jarin yin sana’a, ko kuma idan suna da sana’a, mu taimaka masu da abinda zai kara bunkasa sana’arsu. Wani lokacin kuma mukan taimaka wa yaran ta vangaren biyan kudin makaranta da dai dawainiyar karatu.

Sannan mukan dauki nauyin yara mata, a koya masu hanyar dogaro da kai, kamar koyon na’ura mai kwakwalwa. Sannan a cikin ayyukan mu akwai taimaka wa marasa lafiya masu karamin karfi. Sannan akwai bada shawarwari kamar yadda na fada, sulhu a auren ko kuma masu shirin yin auren. Kuma mukan shirya tarukan wayar da kai, musamman ma ga ‘yanmata.

 A matsayinki ta mace, ko kin fuskanci wani kalubale a lokacin da ki ka yi yunkurin asassa wannan abin alherin?

Eh, ai kamar yadda na gaya miki, a ‘society’ mu, ana ganin duk macen da ba ta yi aure ba, ana mata kallon marar hakuri, ko mai zaman kanta, fitinanniya dai haka wadda ba ta jin magana. To gaskiya a lokacin da na yi shirin yin wannan gidauniyar na fuskanci matsala, a vangaren ‘yan’uwana da na yi ta neman shawarar su, kuma na so su zo mu hada hannu mu yi aikin nan a tare. To alhamdu lillah dai abin ba wani nisa ya yi ba duk suka fahimce ni. Kalubale na biyu da muka fuskanta shi ne, bayan yi wa gidauniyar rijista muka yi ta fafutukar neman inda za mu zauna, wato ofis kenan, saboda aiki irin wannan muna bukatar wurin zama ni da abokan aiki. To sai ya zama idan muna son yin wani metin haka a lokacin sai dai mu samu kamar wurin cin abinci, mu zauna, a tattauna. To wannan ma ba a wani dadewa ba ya wuce.

Sai kuma kalubale na yadda aka yi ta kallon cewa ba zan yi aure ba tunda na shiga wani abu, wanda ake cewa yawancin masu yin sa mata ne da suka gagara, ko ba sa jin magana, zan fara yawon garuruwa da sauransu. To yanzu dai alhamdu lillah na yi auren, kuma Ina zaune lafiya da maigidana, kuma Ina cigaba da ayyukan gidauniyar. Wadannan ne qalubalen da suka zo suka wuce. Masu zuwa a nan gaba kuwa, in sha Allahu mun sha damarar daukar su.

Bari mu fara da zancen mutuwar aure da ki ka yi. Za ki samu mata musamman ma a Kasar Hausa suna shanye duk wani bakin ciki da cin kashi da suke samu a gidan miji, wanda ba don komai suke yin hakan ba, sai don tsoron rayuwar zawarci, hakan kuwa kan iya kai su ga wata varnar ta sava wa Allah. Me za ki ce game da wannan lamarin?

Wannan lamarin na mutuwar aure ba abinda zan fada sai dai na ce, innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na farko dai rayuwar ma gabadaya kaddara ce, kuma ubangiji Ya riga ya rubuta abinda zai faru ga bawa. Kuma Bahaushe na cewa, ita rayuwa kamar karanta littafi ce, idan ka gama da wannan shafi ka tafi na gaba. Don haka duk abinda Allah Ya rubuta zai sami bawa, ba makawa sai ya same shi. Wannan ya kamata mu fara sawa farko, wato mutuwar aure kaddara ce.

Shi ya sa wani lokacin za ki ga an rasa abinda ya kashe wani aure, saboda abin bai taka kara ya karya ba, amma saboda Allah Ya kaddara za a rabun, sai kiga ya kasance. A kullum Ina fada, iyaye su daina rufewa ‘ya’yansu mata kofa, wato kada ka ce da ka yi wa ‘yarka aure ka gama da ita. Ita mace tana rayuwa ne a karkashin kulawa har karshen rayuwarta. Idan tana gidansu tana karkashin iyayenta, idan ta yi aure a karkashin mijinta, idan kuwa aka ce yau ba ta da miji, kulawar ta koma karkashin danta, ko mutanen da ta ke rayuwa tare da su, idan ba ta da da.

To a lokacin da aka ce mace aurenta ya mutu, sai ya kasance ta rasa wannan gatan za ta samu kanta a wata rayuwar da ba a nufe ta da yin irinta ba. Wata za ki ga iyayen ma za su nuna kar ma ta zo gidansu ta ce za ta zauna, don haka sai ki ga wasu sun kama haya, ko in mai abin kanta ce tana da gida sai ta zauna, kinga ta koma karkashin kanta. Kuma a lokuta da dama za ki ga idan an samu rabuwa matan ake bari da dawainiyar yaran.

Wadannan ababe da yawa suke janyo matsaloli. Mace za ta ga idan auren ya mutu ba mai kula da ita, ba mai daukar dawainiyar ta, sannan ga yara, ba mai masu hidima, tarbiyyar su za ta lalace, sannan tana tunanin yadda ma mutane za su dinga kallon ta. Wata ba matsalar daukar dawainiyar ce take kallo ba, domin za ta iya daukar dawainiyar kanta da ta ‘ya’yanta, domin wata ma a gidan mijin nata ma ita ke yin bukatunta da yaranta, amma kallon da za a yi mata a tsakanin al’ummarta na ta qi zaman aure, ko yawon banza ta ke yi. Shi ya sa wata sai ta ga gwara ta hakura ta zauna din. Ba wai don tana jin dadin zaman ba, ko ana sauki hakokkin da Allah Ya ce a bata ba, kawai don ba ta da zavi, ba wanda zai yi tunanin wacce irin rayuwa ta yi a gidan mijin, kawai dai ta ki zaman aure. Babu mace mai hankali da tana zaune da mijinta lafiya, watakila ma har sun haihu ta yi sha’awar su rabu. To yawanci dai irin wannan ke sa matan su hakura su zauna ba don sun so ba, kuma idan aka yi hakan sai ki ga varna ta biyo baya.

Wata idan aka samu mijin ba ya sauke hakkinta ko dawainiyar ta, idan ta samu wani a waje sai su kulla alaka, tana samun bukatunta, kuma tana karkashin inuwar aure, saboda kawai gujewa irin wannan. Kinga kuwa hakan ne babbar barnar.

Dole ne al’umma ta ba wa zawarawa dama su yi rayuwa kamar kowacce mace, domin wadda ta ke zaune gidan miji ba dubarar ta ce ta zaunar da ita ba, ita ma wadda aurenta ya mutu, kaddarar ta ce ta zo a haka.

kin tabo zancen shashancin da matasa da ke jami’o’i ke shimfidawa a rayuwar karatunsu, duk da cewa ba a taru aka zama daya ba, amma duk da hakan akan samu wasu suna yi wa daliban jami’a kudin gora, dalilin kenan da har yau ake samun iyaye ko mazajen da ke kin barin ‘ya’yansu ko matansu karatun gaba da sakandare. Ko akwai wani abu da wannan gidauniyar taku ke yi na wayar da kai, da bambance wa al’umma tsakanin tsakuwa da aya kan lamarin karatun zamani ga matasa mata?

To dama duk inda aka samu mutane sun hadu, za ki samu akwai na kirki akwai kuma bata gari, musamman ma irin haduwar da ake yi a makarantun gaba da sakandare, kusan kowa ma matashi ne, ana ganiyar samartaka ko ‘yanmatanci. Kuma ga dama da suke ganin sun samu, na ba mai matsa maka ka shiga aji, ba mai sa ka saka kayan makaranta.

To wani sai ya ga ya samu ‘yanci ba kamar karamar makaranta da babba ba, domin haka sai ya ga sakewa ta zo mashi, tunda a baya yana a takure ne, yanzu ko zai iya fita lokacin da ya ga dama, ya dawo lokacin da yake so duk da sunan karatu ba tare da iyayen sun fahimci komai ba. To wannan ‘yanci da matasa ke samu, wani lokacin sai ya dan canza masu tunani, maimakon a tsaya a yi abinda ya kamata, sai kuma a hadu da gurbatattun abokane, sai wasu abubuwa su shigo. To amma wannan abu ba yana faruwa a iya makarantun gaba da sakandare ba ne, yana faruwa a ko’ina ma, domin yanzu a yaran da ke unguwa ma, wadanda ba su je makaranta ba ma ana samun masu shaye-shaye, su dami mutane da sace-sace, da rikicin daba.

Su ma matan gasu nan, yau ta shiga nan gidan, gobe a gan ta can gidan biki, yawo ta ko’ina ganin ta ake yi, sai ki samu a irin haka ta hada kanta da shaye-shaye, ko haduwa da samari wadanda ba na kirki ba.

Don haka iyaye su fahimci cewa ita lalacewar tarbiyya ba a iya makaranta ta tsaya ba, don haka nake ba su shawara, kada ya zama dalilin da zai hana su barin ‘ya’yansu su yi karatu ba. Abinda kawai ya kamace su tun farko ya zama sun ba wa ‘ya’yansu ingantacciyar tarbiyya, kuma idan sun tura su makarantun gaba da sakandare ya kasance suna ba su kulawar da ya kamata.

Idan mahaifi ya san ba shi da abin daukar dawainiyar karatun ‘yarsa, to kada ya tura ta. Domin idan ta je makarantar, ya kasance ita ke daukar dawainiyar karatunta, to nan ma an gudu ne ba a tsira ba, dole abinda ba a so din zai iya faruwa. Don haka ni abinda zan ba wa iyaye shawara kuma ni na yarda da shi, ba abinda ya fi a rayuwar mace kamar dora ta kan hanyar neman ilimi, har zuwa lokacin da ta samu miji, idan kuma mijin da ta samu shi ma mai ra’ayin karatun ne, idan ta samu ta gama, idan ya ce ba za ta yi aiki ba, shi kenan ta bari, dama dai ilimin an samu, sai ta nemi wata sana’a ko idan tana yi ta mayar da hankali sosai kanta.

Wacce shawara ki ke da ita ga iyaye mata kan irin rikon sakainar kashi da suke yi da tarbiyyar ‘ya’yansu da sunan zamani?

Za mu kai karkashin wannan tattaunawa a sati mai zuwa da yardar mai dukka. Inda za mu soma da samar da amsar tambayar da muka tsaya kanta, kafin ragowar tambayoyin su biyo baya.