‘Yan bindiga sun sako Shugaban Karamar Hukumar Akwanga bayan biyan kuɗin fansa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Karamar Hukunar  Akwanga a Jihar Nasarawa, Safiyanu Isah Andaha, ya shaƙi iskar ‘yanci bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

An sako shi ne tare da  abokinsa, Adamu Custom da wasu mutum biyu wadanda aka yi garkuwa da su a lokaci guda ranar Litinin da daddare.

MANHAJA ta kalato cewa, sai da aka biya fansar Naira miliyan 10 kafin aka sako wadanda lamarin ya shafa.

Majiya da ta bukaci a dakaya sunanta ta bayyana cewa, an saki wadanda aka yi garkuwa da su din ne a bayan wani gidan mai da ke hanyar Bayan Dutse a yankin Andaha.

Majiyar ta kara da cewa, bayan da aka sako su ne aka kwashe su zuwa asibitin  FMC da ke Keffi don duba lafiyarsu.

MANHAJA ta raito an sace shugaban karamar hukumar ne tare da wani mai suna Alhaji Adamu Tanko Custom da misalin karfe 8:30 na daren Litinin da ta gabata.

By Editor