Gwamnati ta yi watsi da shirin karin kudin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta yi tsayin daka kan kin amicewa da karin farashin wutar lantarki kamar yadda kamfanin samar da lantarki na Nijeriya ya bukata.

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.

Ministan ya jaddada kudurin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatacciyar wutar lantarki a kasa.

Adelabu ya kara da cewa, “Rashin damarmaki na ci gaba da zama babban kalubalen da fannin lantarki ke fuskanta.

“Muna yin nazari kan tsarin aiwatar da jadawalin kuɗin fito tare da tabbatar da ci gaba da ba da tallafin lantarki don amfanin masu karamin karfi a cikin al’umma”, in ji shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahoto ya nuna kamfanoni sarrafa lantarki na shirin karin kudin wutar lantarki a fadin kasa.

 A nata bangaren, Hukumar Kula da Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), ta yi karin haske kan batun, inda ta ce ba ta bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki kowane umarni game da karin kudin wuta ba.