Rundunar sojoji ta yi wa jami’ai 656 ritaya

Daga BELLO A. BABAJI

Sojojin sun yi wa ƙasa hidima ne ta tsawon shekaru 35 inda suka ɗauki watanni shida suna karɓar horon tantancewa kafin yi musu ritayar, a Cibiyar Sansanin Sojojin Nijeriya (NAFRC) dake Oshodi a Jihar Legas.

Sojojin sun haɗa da na ƙasa guda 535 da na ruwa guda 86, da na sama 35 da kuma wasu biyu daga Hukumar Leƙen Asiri (NIA).

A lokacin da ya ke jawabi, Shugaban sojojin Sama, Iya Mashal Hassan Abubakar ya jinjina wa sojojin bisa ƙoƙarinsu da horo da suka samu waɗanda hakan suka yi sanadiyyar yaye su.

Ya ce samuwar rundunar a ƙasa abu ne dake tabbatar da ɗorewa da ci-gabanta, ya na mai cewa za su cigaba da ƙoƙarin inganta harkokin sojoji a Nijeriya.

Ya kuma yaba musu tare da kira a gare su da su kasance jakadun sojoji a garuruwansu.