Saƙon Sakatare-Janar na MƊD a ranar bikin Majalisar Ɗinkin Duniya ta 2024

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Duniya ce ta gina Majalisar Ɗinkin Duniya domin hidimta wa al’ummar duniya.

Tun daga 1945, ya zama an tsara wasu ƙasashe da za su samar da mafita da haɗin-kai don magance matsalolin duniya da samar da zaman lafiya.

Mafitar da za ta kawo sassaucin tashe-tashen hankula, da kuma gina hanyoyin da za su wanzar da zaman lafiya.

Ba wani abu ba ne mafita illa kawar da fatara, da zaburar da ci-gaba mai ɗorewa, da tsayawa wajen ganin an taimaki masu rauni.

Mafitar da ke bada agajin ceton rai ga mutanen da ke rayuwa a yankunan da ke fama rikice-rikice, tashe-tashen hankala, matsalolin tattalin arziƙi da bala’o’in sauyin yanayi.

Mafitar da ke daidaita ma’aunin adalci da daidaito ga mata da ƴan mata.

Hanyoyin da ke magance batutuwan da ba za su iya misaltuwa ba tun daga 1945, canjin yanayi, fasahar dijital, basirar wucin-gadi, da sararin samaniya.

A cikin Satumba, Babban Taron ya amince da yarjejeniya domin ci-gaban Ƙa’idar Dijital ta Duniya da Sanarwa kan Ƙarni mai zuwa.

Waɗannan muhimman yarjejeniyoyin za su taimaka wajen tabbatar da cewa tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya ya daidaita gyare-gyare da sake sabuntawa, don haka ya dace da sauye-sauye da ƙalubalen da ke kewaye da mu da kuma samar da mafita ga kowa.

Amma aikinmu zai kasance a koyaushe mai tushe a cikin ɗabi’u da bin ƙa’idodin Yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya da dokokin ƙasa-da-ƙasa, da kuma mutunta ƴancin ɗan’Adam na kowane mutum.

A cikin duniya mai wahala a yau, har yanzu ba a cimma wannan burina ba

Fatanmu da buƙatar yunƙurin aiki da hanyoyin magance rashin zaman lafiya, wadata juna da bunƙasa duniya.

Burinmu shine, tabbatar da buƙatar duk ƙasashe su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa. Wannan shine abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke buƙata.

A wannan rana ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ina kira ga dukkannin ƙasashe da su kiyaye wannan haske ga duniya, da manufofinta ke haskakawa.

By Babaji