Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Gwamnatin Jihar Katsina ta buƙaci dukkan asibitoci masu zaman kansu da ke aiki a jihar su tabbatar su cika ƙa’idojin da doka ta shinfiɗa ta hanyar sabunta rajistarsu.
Haka kuma an buƙacie su da su tabbatar suna da kayan aiki na zamani,ma’aikata masu ƙwarewa da kayan aikin jinya masu inganci.
Kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya bayyana haka tare da gargaɗin cewa cibiyoyin da suka kasa bin wannan doka za a ɗauki matakan rufe su nan take .
Yace dokar Edict No.5 na shekara 1999 wadda ta tsara ƙa’idojin gudanar da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a Katsina,na ci gaba da aiki sosai,kuma gwamnati ba za ta laminci karya doka ba.
Kwamishinan ya ƙara da cewa nan da mako uku kwamitin da gwamnati ta kafa zai fara cikakken bincike kan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a jihar
Makon da ya wuce, gwamnatin ta bada umurnin rufe cibiyoyin koyon kiwon lafiya masu zaman kansu tare da buƙatar su sake rajista na cibiyoyin ta su.
Wannan matakin da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan bincike da ma’aikatan kiwon lafiya tayi,ta gano cewa mafi yawan cibiyoyin suna aiki babu rajista.
