Sabon cece-kuce ya ɓarke kan mutuwar jarumi Alex Ekubo 

Spread the love

Ya wofantar da mahaifiyarsa, ba mai mutunci a idonsa sai matar ubansa, inji ɗan uwan jarumin 

Daga AISHA ASAS 

Watanni kaɗan bayan rasuwar fitaccen jarumin Nollywood Alex Ekubo, sabon rikici ya ɓarke cikin iyalansa bayan wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin ɗan uwansa, Clinton Ekubo, ya fito da jerin zarge-zarge da suka sake ɗaga hankalin jama’a kan yadda rayuwar marigayin ta kasance kafin mutuwarsa da kuma yadda aka gudanar da jana’izarsa.

A cikin wani dogon saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Clinton ya yi ikirarin cewa matar mahaifin Alexx ta taka muhimmiyar rawa wajen yanke muhimman shawarwari da suka shafi rayuwar jarumin, lamarin da ya ce ya haifar da nesantar danginsa na jini daga gare shi.

A cewar Clinton, Alexx Ekubo ya fara nuna kusanci da dangin matar mahaifinsa fiye da iyalansa na asali, inda ya kan halarci bukukuwa da tarurrukansu, amma ba kasafai yake shiga harkokin danginsa na jini ba.

Ya kuma yi zargin cewa matar mahaifinsa ce ta shirya masa aure da ‘yar wata ƙawarta ba tare da sanin dangin Ekubo Okwareke ba.

A cewarsa, labarin auren ya zo wa iyalan a bazata, domin ba a sanar da su kafin a gudanar da shi ba.

Haka kuma, Clinton ya yi iƙirarin cewa Alexx bai da kusanci da ƙanwarsa ta jini, Chioma, yayin da ya fi mu’amala da ‘ya’yan matar mahaifinsa.

Clinton ya ci gaba da cewa marigayin ya daina hulɗa da mahaifiyarsa ta jini tun tana raye, yana mai cewa har zuwa lokacin rasuwarsa, dangin ba su san cewa yana fama da rashin lafiya ba.

Ya ce sanarwar mutuwar Alexx ta zo musu ne a matsayin babban abin mamaki duk da firgici, domin a cewarsa sun ji labarin ne bayan an sanar da jama’a.

Clinton ya kuma nuna damuwa kan yadda aka gudanar da jana’izar jarumin, yana mai cewa an yi gaggawar shirya komai.

Ya yi ikirarin cewa abokai da matar mahaifin Alexx ne suka jagoranci shirye-shiryen jana’izar, yayin da ya ce dangin marigayin ba su taka rawar da ta kamata ba.

Har ila yau, ya yi zargin cewa lokacin da ya ga gawar Alexx, ya lura da abin da ya bayyana a matsayin tarin jini a ɗaya daga cikin idanunsa, lamarin da ya sa yake neman a yi ƙarin bayani kan abin da ya faru kafin mutuwarsa.

Ya kuma ce sun ji cewa an kai jarumin asibiti ne bayan ya riga ya rasu, yana mai cewa wannan da sauran abubuwan da suka faru sun bar iyalan da tambayoyi masu yawa.

Ya ce “Ahalinsa na neman gaskiya, ba dukiya ba.”

Clinton ya jaddada cewa manufar fitar da waɗannan zarge-zarge ba neman gadon marigayin ba ce.

A cewarsa, abin da iyalan Ekubo Okwareke suke nema shi ne cikakken bayani kan abubuwan da suka kai ga mutuwar Alexx da kuma dalilan da suka sa aka gudanar da wasu matakai ba tare da cikakken sa hannun danginsa ba.

Ya kuma soki irin tasirin da ya ce matar mahaifin Alexx ke da shi a cikin iyalin, yana mai cewa hakan ya saɓa wa al’adun Igbo.

An sanar da rasuwar Alexx Ekubo ne a watan Mayu bayan iyalansa sun bayyana cewa ya rasu a Asibitin Evercare sakamakon cutar sankarar ƙoda mai tsanani wadda ta bazu zuwa wasu sassan jikinsa.

An yi jana’izarsa a ranar 18 ga Yuni, inda manyan jaruman Nollywood, abokansa da masoya suka halarta domin yi masa bankwana na ƙarshe.

Duk da zarge-zargen da Clinton Ekubo ya yi, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto babu wata sanarwa daga matar mahaifin Alexx Ekubo ko sauran iyalansa da ta mayar da martani kan waɗannan iƙirari.

By ukarofi

Leave a Reply