Sai da aka biya miliyan N50 kafin sako alƙalin Kebbi, inji iyalansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruk Hassan Bunza da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a gidansa, sun tabbatar da cewa sai da aka biya kuɗin fansa Naira miliyan 50 kafin aka sako shi.

Rahotanni sun bayyana cewa, Alƙali Bunza ya shaƙi iskar ‘yanci ne a ranar Litinin bayan shafe kwanaki takwas a hannun ‘yan bindigar da suak sace shi a safiyar ranar Lahadi, 26 ga Yuli, lokacin da suka je gidansa da ke Ƙaramar Hukumar Bunza a jihar Kebbi.

Wani ɗan gidan alƙalin da ya nemi a sakaye sunansa saboda ba a ba shi izinin magana kan al’amarin a fili, ya tabbatar wa Daily Trust cewa miliyan N50 aka biya masu garkuwar kafin suka bayar da jojin.

Ya bayyana cewa, a halin yanzu mai shari’ar yana karɓar kulawar tare da cigaba da warkewa daga halin rashin lafiya da yake ciki.

A cewarsa, da fari ‘yan bindigar sun nemi a biya miliyan N200 ne a matsayin kuɗin fansar, amma daga bisani sun karɓi N50m bayan kwanaki ana tattaunawa da su.

Ɗan ahalin ya kuma miƙa godiyarsa ga gwamnatin jihar Kebbi, hukumomin tsaro, fannin shari’a da mazauna jihar bisa addu’o’i da gudummawar tallafi da suka bayar yayin da alƙalin ke komar ‘yan bindigar.

Kazalika, wani ɗan gidan ya shaida wa DCL Hausa cewa ‘yan ta’addar, waɗanda ake kyautata zaton su biyar ne, sun karɓi kuɗin ne a ranar Juma’a bayan sun umarci iyalan da su kai kuɗin wani waje a jeji mai nisan kilomita 70 daga Birnin Kebbi.

By Babaji

Leave a Reply