
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, ta kammala bincikenta akan cece-kucen badaƙalar wanzuwar Hukumar kula da Ci-gaban Zuba Jari na Ƙasashen Waje ta Shugaban ƙasa (PFIPC).
Haka kuma, kwamitin binciken al’amarin na wucin-gadi na Majalisar Wakilai ya ce zai ba wa ‘yan Nijeriya ba’asin sakamakon binciken a wannan mako gabanin miƙa rahotonsa ga majalisar, bayan tsawon makonni ana binciken akanHukumar.
A ranar 7 ga Yuli, 2026 ne Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC da ta gudanar da cikakken bincike akan PFIPC cikin kwanaki 30 tare da bayar da rahotonta domin gano haƙiƙanin yadda al’amarin yake.
Majiyoyi daga ICPC sun shaida wa Daily Trust cewa ainihin wanda ake zargi kan cece-kuce, Frins Adeniyi Adeyemi, wanda aka kira da darakta-janar na PFIPC, an ƙaddamar da cikakken bincike akansa, ƙarƙashin jagorancin sashen leƙen asiri (IRT) a ofishin jami’ai na musamman kan yaƙi da miyagun laifuka (SARS), a yankin Guzape da ke Abuja, inda a yanzu haka yana hannu tun bayan umarnin kama shi.
Yunƙurin ji ta bakin kakakin ICPC, John Odey bai yi nasara ba yayin da ake ƙoƙarin samun bayanai a hukumance kan al’amarin.
Saidai duka da wannan ci-gaba, Adeyemi ya roƙi kwamitin majalisar da ya ba shi damar zuwa gabansa domin bayar da ba’asi na kai tsaye, yana mai cewa dukkan wani bayani da za bayar akansa ba tare da ji ta bakinsa, zai zama tauye masa ‘yanci kamar yadda tawagar lauyoyinsa suka bayyana ƙarƙashin jagorancin Festus Akhigbe.
