Sai na sanya hawan jini ga maƙiyan Tinubu – Wike

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin ci gaba da haddasa hawa jini ga waɗanda ke adawa da Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ayyukan alheri da shugaban ƙasar ke aiwatarwa tun bayan hawansa mulki a 2023 ne ke sa su cikin baƙin ciki.

Wike ya bayyana hakan ne yayin buɗe wasu sabbin hanyoyi a yankin Katampe da shugaban ƙasa ya jagoranta.

Ya ce ya lura da irin ƙin jinin da wasu ke yi wa Tinubu ne lokacin da yake kallon talabijin, inda ya fahimci cewa wasu ba sa farin ciki da ci gaban da ake samu a mulkin shugaban.

Saboda haka, ya sha alwashin ci gaba da gabatar da ayyukan ci gaba da za su kara tayar wa da maƙiyan shugaban hankali.

A cewarsa: “Na ji kamar wani abu ne ya motsa ni a ruhi na sai na kunna talbijin, sai na ga wasu na cikin raɗaɗi saboda ci gaban da ake samu. Yanzu na gane suna cikin ciwo, kuma zan tabbatar ina sa musu hawan jini.

Mu muna dariya, su kuma na fama da zafi. Wannan yanzu shi ne aikina.”

By ukarofi