Ranar Dimukraɗiyya: Tinubu ya soke jawabin safe, zai gabatar a zauren majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya soke yin jawabi ga ƴan Nijeriya a safiyar Alhamis kamar yadda aka tsara da farko domin karrama Ranar Dimukraɗiyya a karo na 26 a ƙasar.

A sanarwar da Daraktan yaɗa labaransa, Segun Imohiosen ya fitar a sa’o’in ƙarshe na ranar Laraba, ya ce a madadin haka Shugaban ƙasar zai halarci zaman haɗaka na Majalisar Dokoki.

Ya bayyana cewa, Tinubu zai gabatar da jawabinsa na bikin Ranar Dimukraɗiyya daga zauren Majalisar da misalin ƙarfe 12 na rana.

Sannan ya kuma ce, sauran abubuwan da aka tsara, za a gudanar da su ba tare da sauyi ba.

Da farko an sanar da soke gudanar da faretin sojoji, wanda kawo yanzu ba a san dalilin yin hakan ba.

Haka kuma, za a gabatar da lakca mai taken ‘Consolidating on the Gains of Nigeria’s Democracy: Necessity of Enduring Reforms’, da misalin ƙarfe 4 na yamma a ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa, wanda ƴan jaridar da ke aiki a Fadar ne kaɗai aka amince su ɗauki rahotonta.

By Babaji