Na yarda dari bisa ɗari cewa aikin hajjin kiran Allah ne don ba matukar dagewar mutum kan sa shi sauke faralin aikin hajji ba. Akwai masu tarin dukiya da ke komawa ga Allah ba tare da sun samu gudanar da aikin hajji ba. Wasu ma a garin Makkah su ke amma sai ba za su samu gudanar da aikin hajji ba. Mu na cikin kwanaki goma na watan Zhulhijjah inda a ke gudanar da aikin hajji. Da tsada ko ma yaya ma za a ce an sake tara ɗimbin Musulmi da ke gudanar da aikin hajjin na hijira 1446 daidai 2025 miladiyya. Malamai sun tabbatar ma na cewa Manzon Allah mai tsira da aminci sau daya tak ya taba gudanar da aikin hajji wato hajjin nan na sa na bankwana inda ya gabatar da huduba don al’ummar sa su ɗore kan hakan don samun rabo na alheri a duniya da gobe kiyama. A nan dai ina son nuna cewa ko mutum ya na da guzurin zuwa aikin hajji to said a rabon zai iya gudanar da aikin. Ko a bana Dokta Ahmed Gumi da ke cikin manyan malamai na Nijeriya ya daura haramar gudanar da aikin hajji amma Allah bai hukunta a bana zai iya yin hakan ba don an juyar da shi ya komo gida daga filin saukar jiragen sama na Yarima Muhammad da ke Madina. Wasu ma maniyatan Allah bai hukunta za a yi hawan arfa da su ba don tun a ziyarar Madina rai ya yi halin sa. Wannan ibada ta aikin hajji ta wajaba ne kan Musulmi mai dammar yin hakan sau ɗaya a rayuwa in mutum ya samu dama daga baya sai ya zama kamar nafila.
Don haka ya na da kyau duk wanda ya samu dama ya gudanar da aikin hajji matuƙar ya na da guzuri da lafiyar yin hakan. Ibada ce da haƙiƙa in mutum ya samu dammar zuwa zai iya samun ƙarfin imani da cudanya da dubban musulmi daga dukkan faɗin duniya masu Magana da harsuna daban-daban amma duk sun yi imani da Allah shi daya ne Annabi Muhammadu Manzon Allah ne. A cikin Alƙur’ani Allah ya baiyana halittar mutane daga maza da mata da rarraba su a kabilu da ƙasashe don su san juna amma a nan madaukakin Sarki ya cikata ayar da “wanda ya ke ɗaukakke a cikin ku shi ne wanda ya fi tsoron Allah” Da zuwan aikin hajji mutum zai gane hakan na bambancin mutane da ke taru a waje ɗaya don ibada ɗaya ga farare ga baƙaƙe ga dogaye da gajeru duk bayin Allah ne. Siffar halittar jiki ba ita ke zayyana girman darajar mutum ba amma a na duba ƙarfin imanin mutum ya ke a wajen bin dokokin Allah. Na taɓa jin wasu na misali da baƙar rigar ɗakin Ka’aba da su ke nuna hakan daraja ce ga bakar fata don ba mamaki hakan ya zama misalin jan hankalin farare masu raina baƙar fata. A nan duk ba a ma buƙatar mutum ya duba kalar fatar sa amma ya shiga zuciyar ya gwada mizanin tsoron Allah da ya ke da shi.
A zamanin Manzon Allah an yaki duk wata wariya ko nuna bambanci na jinsi ko wata alfarma da wani ya ke tinƙaho da ita.Sayyid Bilal wanda bakar fata ne kuma asali ma bawa ne daga Habasha ya zama mai matuƙar daraja a tsakanin sauran sahabbai Larabawa don yanda ya rike addinin Musulunci. Shi ne ladanin ma’aikin Allah. Har gobe Sayyid Bilal na daga sahabbai da a ke tunawa da gagarumar gudunmawar su ga addinin Allah. A birnin Madina na wajajen anguwar Kurban akwai masallacin Bilal da kan tunawa mutane wannan babban sahabi. Duk yanda musulmi zai yi ya tabbatar ya fifita dangantaka ko ‘yan uwantakar addini fiye da ta kabila. A nan ba ma ƙabilanci kaɗai a ke nuni da shi ba a’a hatta ka ɗau wani mutum shi ne mafi girman kusaci da kai don ƙabilar ku daya. Dangantakar addini ita za ta ƙarfafa adalci da riƙon amana. In mun duba biyewa bambancin fata ko ƙabila duk hanyoyi ne da kan kai mutane ga rashin adalci don su kan fifita son zuciya da yadda gaskiyar lamari ya ke. In mun riƙi alaƙar addini sau da kafa to za mu samu dauwamar zaman lafiya da mutunta juna. Addini na da dokoki ne ko in ce umurni daga Allah da ya halicci sammai da ƙassai. Bin dokokin nan kan inganta rayuwar al’umma su riƙe kare haƙƙoƙin juna. Da zarar an kaucewa hakan za a iya faɗawa tarkon son zuciya. Shi kuma son zuciya ba ruwansa da adalci, hasalima yaƙi ya ke yi da duk nau’in adalci don yadda zuciya kan rayawa mutum ya ba wa marar gaskiya gaskiya kuma ba tare da tunanin hakan zalunci ba ne.
Ziyara zuwa Madina kan sauya mutum don sabuwar natsuwa da zai iya samu lokacin da ya shigo birnin Manzon Allah. A Madina ne ma’abota motoci kan tsaya cak a kan titi don barin masu wucewa da kafa su tsallake. Hakan na faruwa ne hatta a inda ba alamar nan ta tsallakewa. Abu biyu ke jawo ma’abota motoci mutunta masu tafiya a kafa na farko mutunta ɗan adam da Allah ya fifita da kuma musamman gari ne da baki kan shigo don ziyartar Manzon Allah don haka sun cancanci karramawa. Na biyu shi ne dokar Musulunci da za ta ɗau mataki kan wanda ya kaɗe wani da gangan inda za a iya samun asarar rai. Sauran wajajen ziyara musamman maƙabartar Baki’a inda dubban bayin Allah ke kwance ciki da Khalifan Manzon Allah Usman bin Affan, matan Manzon Allah, sahabbai da ma babban mufti na Madina Imam Malik Dan Anas. Duba darajar waɗannan bayin Allah da ke kwance a maƙabartar nan zai sa mai imani tuna haƙiƙa wataran shi ma zai shiga wannan rami kuma ba shi da abokai da za su deɓe ma sa kewa sai aiyukan san a alheri.
Masallacin Kuba mai darajar da sallah a cikin sa za ta samawa mutum ladar umrah. Ga Uhudu inda manyan sababbai da su ka yi shahada a yakin Uhudu ke kwance ciki kuwa da Sayyid Hamza, Lallai idanu ka iya zubar da hawaye. Ga Kandak inda a ka tona rami don kare birnin Madina daga kutsen abokan gaba a yaƙi. Wannan waje ya na cike da tarihi na majalisu daban-daban na rundunar musulunci. Ga rijiyar Gaz da aka ba da labarin Manzon Allah kan sha rowan ta kuma da ruwan a ka yi ma sa wanka lokacin da ya yi wafati. Sai kuma uwa uba mutum ya shiga masallacin Manzon Allah inda gidan sa ya ke da kuma makwancinsa tare da manyan sahabban sa Sayyid Abubakar da Umar. Ciki a ke da Rawda da Manzon Allah ya ce tsakanin gidan sa da Mumbarin sa a ke da wannan bigire na aljannah. Masu ziyara kan yi shauƙin shiga wannan muhalli don yin addu’o’I na musamman. Abu mai muhimmanci shi ne koyon haƙuri da juna a lokacin wannan ibada da ta yi bambanci da tafiya ta yawon buɗe ido don wannan ibada ce zallah kuma da ke bukatar lafiyar jiki. Ko ban faɗa ba an ba wa duk wanda ya samu kan sa a dammar gudanar da hajji ya isa filin arfa ranar 9 ga watan na Zhulhijjah kuma ya yi amfani da darajar filin wajen yin addu’o’i na neman rabauta duniya da gobe kiyama.
Sheikh Pakistan Na Aikin Da Ya Kamata A Hukumar Nahcon – Sheikh Bala Lau:
Shugaban ƙungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yaba wa sabon Shugaban Hukumar Alhazai Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan don yadda a ka gudanar da jigilar alhazai ba tare da tangarɗa ba.
Sheikh Bala Lau na zantawa da manema labaru ne a Madina gabanin fara gudanar da aikin hajjin bana.
A nan Sheikh Lau ya ce nada malami mai wa’azi a matsayin jagoran hukumar alhazai farar dabara ce don yadda aikin hajji ya ke rukuni a Musulunci.
Malamin ya buƙaci malamai da sauran jama’a su taya Sheikh Pakistan da addu’a don ɗorewa da nasarorin da ya samu a wannan aiki da ya shafi dubban musulmi.
Kazalika malamin ya shawarci alhazai waɗanda su ka kasha miliyoyin Naira don zuwa aikin hajji su yi amfani da dammar wajen yi wa kan su, iyalan su da ƙasar su addu’ar samun taimakon Allah.
Kammalawa;
Yayin da a ke ƙoƙarin gudanar da aikin hajjin na bana can kuma Gaza akwai alamun samun sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta duk da kullum mu kan ce ba girin-girin ba ta yi mai. ƙungiyar Hamas mai mulkin Zirin Gaza na buƙatar wasu gyare-gyare a sabuwar yarjejeniyar neman tsagaita wuta tsakanin ta da Isra’ila.
Wannan yarjejeniyar na ƙarƙashin kulawar Amurka inda a nan jakadan shugaban Amurka Donald Trump wato Steɓe Witkoff ya ƙi amincewa da neman gyaran.
Duk da haka Hamas ba ta yi tsauri a kan martanin na Witkoff ba don burin ta na neman kawo ƙarshen yakin gaba ɗaya da ya faro tun 7 ga Oktobar 2023.
Hamas na buƙatar janye sojojin Isra’ila daga Gaza kakaf da hakan zai ba da damar tulalowar kayan agaji ga jama’ar yankin masu matuƙar buƙatar taimako.
Idan yarjejeniyar ta kwana 60 ta cimma nasara, Hamas za ta miƙa mutum 10 daga kamammun Isra’ilawa da ke hannun ta da wasu gawawwaki 18 cikin adadin sauran kamammun 58 da ke hannun ta.
Za a yi fatan samun ɗorewar wannan yarjejeniya a wannan karon don aƙalla a rage zubar da jinin mata da ƙananan yara a Gaza.
