Sakatare Janar na OPEC, Barkindo ya kwanta dama

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sakatare-Janar na Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Man Fetur OPEC, Muhammad Sanusi Barkindo, ya riga mu gidan gaskiya.
Barkindo ya rasu a ranar Talata da misalin ƙarfe 11 na dare yayin da yake da shekaru 63 a duniya kamar yadda Mele Kyari ya sanar.

Barkindo shine tsohon GMD na NNPC na uku da ya rasu cikin shekaru biyu bayan Maikanti Baru da Joseph Dawha.

Mele Kyari, Manajan-Daraktan Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPC, ya bada sanarwar mutuwarsa a wallafarsa ta Tiwita a sa’o’in farko na ranar Laraba.

Ya kuma kwatanta rasuwarsa da babban rashi ga iyalansa, NNPC Nijeriya, OPEC da duniya baki ɗaya.

“Mun yi rashin Dr. Muhammad Sanusi Barkindo. Ya rasu wurin ƙarfe 11 na daren jiya (Talata) 5 ga watan Yulin 2022.

“Babu shakka wannan babban rashi ne ga iyalansa, NNPC, ƙasarmu ta Nijeriya, OPC da duniya baki ɗaya,” kamar yadda Kyari ya wallafa a tiwita.

Kyari ya cigaba da cewa, “za a sanar da shirin jana’iza nan ba da daɗewa ba.”

Barkindo shi ne na uku a cikin tsofaffin GMD na NNPC da ya rasu a cikin shekaru biyu. Maikanti Baru ya rasu a watan Mayun 2020, sai Joseph Dawha ya rasu a watan Augustan 2020.

By Editor