Samar da adalci a shari’a: Gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da ƙananan kotunan shari’a 

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 

Gwamnatin Jihar Zamfara ta hanyar tallafin shirin SABER, ta ɓullo da wata ƙaramar kotu a cikin tsarin shari’ar jihar da nufin samar da adalci a tsakanin marasa galihu a jihar a ɓangaren sharia.

Kotun za ta taka rawar gani wajen inganta samar da adalci wajen gunar da shari’o’i don tabbatar da adalci akan lokaci a jihar. 

Babban Lauyan jihar kuma babban sakatare na ma’aikatar shari’a Musa Garba Bukkuyum ne ya bayyana haka a wajen taron wuni ɗaya na masu ruwa da tsaki na sake duba ƙudirin dokar jihar Zamfara na kafa wata cibiyar magance rigingimu da aka gudanar a Command Guest Inn Gusau Litinin wanda ƙungiyar International Alert ta shirya. 

Sani Garba ya ci gaba da cewa, hanyoyin da aka kafa ta hanyar gudanar da aikin kotun wanda Mai Shari’a Kulu Aliyu OFR, ta ba da ƙwarin guiwa, Gudanarwa tare da inganta amfani da magance rikici a tsakanin masu ƙara, tare da yin shari’a a matsayin mafita ta ƙarshe.

A nashi jawabin Daraktan ƙasa da ƙasa na International Alert, Dr. Paul B. Yulaku ya bayyana cewa, maƙasudin gudanar da taron shi ne a wayar wa da masu ruwa da tsaki yadda harkar shari’a ke gudana dare da tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar wajen magance rikice-rikice.

Ya ce ƙungiyar ta International Alert tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara da masu ruwa da tsaki za su cigaba da bayar da muhimmanci wajen tabbatar da samar da adalci da kuma sauƙaƙa hanyoyin magance rikici a a tsakanin al’umma a jihar.

A cewarsa, shugabannin addinai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, za su haɗa ƙarfi da ƙarfe da ƙungiyar ta International Alert domin bayar da shawarwarin tabbatar da adalci da yaƙi da cin zarafin mata a jihar. 

Dokta Paul ya ci gaba da cewa, International Alert za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da ƙudirin dokar samarwa da kafawa, gudanarwa, tsarin mulki da kuma ayyukan cibiyar magance rikice-rikice ta jihar Zamfara domin bai wa ‘yan ƙasa damar samun adalci a koyaushe.

By ukarofi