Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Malam Yusuf Yakubu wanda aka fi sa ni da O Yes mai sana’ar sayar da dambun nama a wajen tarurruka da kasuwanni a Kano, ya bayyana cewa a matsayinsa na dattijo wanda ya yi shekara da shekaru kuma yana wannan sana’a ta sayar da soyayyen nama da dabun nama wannan sana’a ta masa riga da wando na arziki domin kuwa ya gina gida yaɗau nauyin ɗawainiyar makarantar yayansa manya da ƙanana na yau da kullum da kuma nauyin hidimar gida da taimakawa ‘yan uwa da maƙota dai dai gwargwado to wannan Sanaa ba ƙaramin rufin asiri ya samu kuma yake samu a kanta ba har yanɗu don haka wannan abun alfahari ne kuma abun farin ciki ne inda kuma ya shawarci matasa da sauran al’umma da kada su yarda su raina sana’a komai ƙanƙantarta domin Sanaa ko kasuwanci sirri ne, Allah kaɗai yasan inda arzikin bawa ya ke don haka a dage a dogara da sana’a da addu’a don samun taimakon Ubaangiji a kowani lokaci.
Haka kuma ya ce a wannan sanaar a can baya a shekarar 2011 zuwa 2015 gwamnan Kano na wannan lokacin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda sanaarsu ta bunƙasa don haka akwai buƙatar yanzu haka Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kallesu da Idon Rahama ya tallafa musu domin buƙasa wannan sana’a kamar dai yadda dattijo Alhaji Yusuf Yakubu wanda aka fi sa ni da O Yes ya nemi tallafi daga gwamnan Abba Kabir Yusuf ganin yadda yake taimakawa masu sanaoi maza da mata da ma sauran alumma.
A ƙarshe ya nemi alumma da cigaba da addua neman ƙarin zaman lafiya da ƙarin arziki a Kano da Nijeriya baki ɗaya musamman a wannan lokaci da mulkin siyasa ya shekara 26 ana yi ba tare wata tanƙarɗa a dumukuraɗiya ba.
