Sanata Marafa ya fice daga APC

Spread the love

Sanata Kabiru Garba Marafa, tsohon dan majalisar dattawan tarayya daga Jihar Zamfara, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC.

Sanarwar haka ta jawo cecekuce a siyasar Zamfara da ma arewacin Nijeriya, ganin matsayin Marafa a jam’iyyar tun kafuwarta har zuwa lokutan da ta samu nasara a jihar.

Da yake bayyana dalilan da suka sanya ya yanke shawarar barin jam’iyyar, Marafa ya yi zargin cewa shugabannin APC a matakai daban-daban sun nuna masa rashin adalci.

Ya ce, duk da irin rawar da ya taka wajen ganin jam’iyyar ta karfafa gindinta a Zamfara, musamman a lokacin da take da karfin fada a ji a jihohin arewa maso yamma, an yi watsi da shi tare da kulle masa hanya a lamurran siyasa.

Marafa ya bayyana cewa ya daɗe yana nuna haƙuri da irin wannan hali da jam’iyyar ta nuna masa, amma yanzu lokaci ya yi da zai dauki mataki domin kare mutuncinsa da kuma ci gaba da gwagwarmaya ta siyasa.

Saidai a yanzu bai bayyana jam’iyyar da ya nufa ba. A cewarsa, “Nan da wani lokaci kadan zan bayyana matsayata a fili. Na yanke shawarar cigaba da fafatawa kai tsaye a siyasa, domin wannan hanya ce ta nuna kishin jama’a da kare muradun talakawa.”

Masu sharhi a siyasar Zamfara na ganin cewa ficewar Marafa daga APC na iya sake sauya taswirar siyasa a jihar, ganin irin masoyan da yake da su musamman a yankin Zamfara ta Tsakiya.

Wasu na ganin akwai yiwuwar ya koma PDP ko kuma shiga wata sabuwar jam’iyya domin cika burin sa na sake taka rawar gani a siyasar jihar da Najeriya baki daya.

By Babaji