Ƙarin kuɗin fasfo: Ba ku damu da wahalhalun al’umma ba – Peter Obi ga gwamnatin Tinubu

Spread the love

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya caccaki Gwamnatin Tarayyar Najeriya kan ƙarin kudin fasfo da Hukumar Shige da Fice (NIS) ta sanar.

A cewar sanarwar NIS, daga 1 ga Satumba, 2025, sabbin farashin fasfo sun kai N100,000 ga takardar shafuka 32 mai ingancin shekaru 5, sai kuma N200,000 ga takardar shafuka 64 mai ingancin shekaru 10.

Farashin zai shafi waɗanda ke neman fasfo a Najeriya kawai, yayin da kuɗaɗen wajen kasar suka tsaya a $150 da $230.

Obi, cikin rubutun da ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana karin kudin a matsayin “tsantsar rashin tausayi” a lokacin da al’umma ke fama da matsanancin wahala.

Ya ce, “wannan shi ne karo na uku a cikin shekaru biyu kacal da aka ƙara kuɗin fasfo. Yanzu farashin ya zama abin da ma’aikaci talakawa ba zai iya ɗauka ba.”

Obi ya ƙara da cewa, “a ƙasar da sabon mafi karancin albashi ke naira 70,000, farashin fasfo daya ya fi albashin ma’aikaci na wata daya. Wannan abin takaici ne kuma alamar rashin alaka tsakanin gwamnati da talakawa.”

Ya kuma roƙi gwamnati da ta sake tunani kan wannan mataki, yana mai cewa, “Maimakon sauƙaƙa rayuwa, ana ci gaba da dora nauyi a wuyan talakawa”, inji shi.

By Babaji