BBC ta ƙi karɓar murabus daga editan sashen Hausa, Aliyu Tanko

Spread the love

Gidan yaɗa labarai na Birtaniya, BBC, ya ƙi amince wa murabus ɗin Editan Sashen Hausa, Aliyu Abdullahi Tanko, bayan da ta dakatar da shi na tsawon watanni uku bisa zargin cin zarafi a wurin aiki da wasu tsoffin ma’aikata suka yi.

Tanko, wanda aka ruwaito an dakatar da shi a ranar Laraba, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Alhamis, amma hukumar ta ki karɓa.

BBC ta gamu da suka sosai bayan wani faifan bidiyo ya yadu, inda tsohuwar ma’aikaciyarta, Halima Umar Salah, wadda ta bayyana a wani shiri a Arewa24, ta yi ikirarin cin zarafi a wurin aiki a cikin hukumar, duk da cewa ba ta ambaci suna ba, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wata majiyar ta daban ta bayyanawa jaridar yanar gizo ta SolaceBase cewa, an ki amincewa da murabus din Tanko ne saboda bai bi ka’ida ba.

A cewar majiyar: “An ki amince da murabus din bisa cewa bai bi tsarin doka ba, wato a matsayin babban jami’i, dole ne ya bayar da sanarwa na akalla watanni biyu kafin ya bar aiki ko kuma ya biya albashin watanni biyu a matsayin diyya, kafin hukumar ta sallame shi.”

Hukumar ta kuma kafa kwamitin bincike kan korafe-korafen da wasu tsoffin ma’aikata da kuma wadanda har yanzu ke aiki a sashen Hausa suka sa hannu a kansu game da tsohon Editan, Tanko.

A cewar SolaceBase, mataimakin babban jami’in gudanarwa na BBC News kuma Daraktan BBC News Global, Jonathan Munro, shi ne ya bayar da umarnin a gudanar da binciken kamar yadda Jaridar Daily Trust ta Rawaito.

By Babaji