Saraki ga ‘yan Nijeriya: Ramadan makaranta ce, mu siffantu da darussan da muka koya

Daga Aisha ASAS, Abuja

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya taya ɗaukacin al’ummar musulmin Nijeriya murnar kammala azumin Ramadana na wannan shekara ta 2021, tare kuma da yi musu barka da sallah.

Saraki a wata takardar manema labarai, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen ofishin watsa labaransa, Yusuph Olaniyonu ya shawarci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da neman kusanci ga Allah tare da yin addu’ar samuwar mafita ga Nijeriya.

Ya ƙara da cewa, watan azumin Ramadana ba kawai ya taƙaita ga kyautata halaye na tsawon kwanaki 30 ba ne, lokaci ne da ya kamata mu sauya halayenmu zuwa masu nagarta.

Ya ce: “Ya kamata mu yi bankwana da duk wasu munanan ɗabi’u da muke da su kafin zuwan Ramadan, mu zama managarta kuma masu kishin kasa wadanda ke yi wa ƙasa addu’a a kodayaushe, don a samu hadin kai, adalci da zaman lafiya.

“Halin da kasarmu Nijeriya ke ciki na bukatar kowannenmu ya canza kansa. Mu yi amfani da darussan da muka koyo daga makarantar Ramadana wurin yin watsi da duk wata dabi’a da muka san ba ta kirki ba ce. Nijeriya ta fi bukatar addu’o’inmu a irin wannan lokaci fiye da koyaushe.

“Bisa la’akari da rashin tsaro da ake fama da shi da kuma yawaitar talauci, dole ne mu hada kai wurin nuna kishin kasa don tsamo Nijeriya daga halin da take ciki.” Inji shi

Daga karshe Dr. Saraki ya yi addu’a ta musamman ga jami’an tsaro, musamman wadanda ke bakin fama don bayar da kariya ga Nijeriya. Ya yi addu’ar Allah Ya ci gaba da basu nasara a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *