Saraki ya musanta kamun da aka ce EFCC ta yi masa

Spread the love

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya musanta labarin da aka yaɗa kan cewa hukumar EFCC ta cafke shi a ranar Asabar da ta gabata.

Saraki ya musanta labarin ne cikin wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Yusuph Olaniyonu, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta nuna cewa, Saraki da kansa kuma a ganin damansa ya ziyarci ofishin EFCC ɗin domin ƙarin bayani kan batun da EFCC ke neman ɗagawa a kansa, amma ba kama shi aka yi ba kamar yadda aka yaɗa.

Ofishin ya ce da yake da ma dai akwai wani kwantaccen batu da ya shafi Sarakin a Babbar Kotun Abuja tun zamanin tsohon shugaban EFCC wanda ya hana hukumar ta bincike shi wanda ya kai ga hukumar ta roƙi kotu kan batun don ta samu zarafin gudanar da bincike kan Sarakin, hakan ya sa Sarakin da kansa ya ziyaci EFCC don amsa mata tambayoyi.

Don haka Olaniyonu ya ce Saraki ya tafi ofishin EFCC inda ya tabbatar mata da cewa shi babu abin da yake ɓoyewa, kuma a shirye yake ya gabatar da kansa duk lokacin aka buƙace shi don ƙarin haske.

“Yanzu haka Dr Saraki yana gidansa,” in ji Olaniyonu.

By Editor