Hukumar Kula da Aikin Ɗan Sanda (PSC), ta amince da a dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, DCP Abba Kyari, bisa zargin karɓar rashawa da Cibiyar Binciken Sirri ta Amurka (FBI) ta yi masa.
Shugaban sashen yaɗa labarai na PSC, Ikechukwu Ani, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ran Lahadi a Abuja.
Haka nan, Mr Ani ya ce hukumar ta umurci Babban Sufeton ‘Yan Sanda, Usman Alkali-Baba, da ya ba ta cikakken bayani kan lamarin don sanin mataki na gaba da ya kamata a ɗauka.
Kamfanin Dillanci Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ‘yan lokutan nan baki ɗaya kallo ya koma kan Abba Kyari wanda fitaccen ɗan sanda ne da ake yi wa kallo da sanin makamar aiki tun bayan da FBI ta zarge jami’in da karɓar rashawa.
Ani ya ce amincewa da a dakatar da Kyari da hukumar ta yi, hakan ya faru ne sakamakon wasiƙar da ta samu daga Sufeto-Janar mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Yuli.
Ani ya ci gaba da cewa matakin dakatar da Kyarin ya soma aiki ne daga ranar 31 ga Yuli, wanda zai ci gaba da zama a haka har zuwa lokacin da za a fitar da sakamakon binciken zargin da aka yi masa.
Haka nan, ya ce an isar wa Sufeto-Janar da matakin da hukumar ta ɗauka cikin wata wasiƙa mai lamba PSC/POL/D/153/vol/V/138 a ranar 1 ga Agusta, wadda kuma ta sami sa hannun Jastis Clara Ogunbiyi, Kwamishina na 1 a hukumar PSC a madadin shugaban hukumar, Musiliu Smith.
