Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu
Sakamakon ci gaba da samun zaman lafiya a Arewa-maso-gabas tare da ma jihar Yobe baki ɗaya, ‘yan ƙungiyar wasan Badminton Damaturu sun shirya wasan sada zumunta a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Da yake jawabi wajen buɗe wasan a ranar Asabar, shugaban kwamitin shirya wasan, Alhaji Bashir Baba Geidam, ya bayyana cewa sun shirya wasan ne domin sada zumunta a birnin Damaturu.
Haka kuma, ya ce wannan wasa an saba gudanar da shi ta haɗin gwiwa tsakanin manyan ɓangarorin badminton da ke jihar Yobe, waɗanda suka ƙunshi na Gashuwa, Postiskum da Damaturu a jihar.
Bugu da ƙari, Geidam ya ce an tsara wasan ne domin a haɗu a yi mu’amala, tattaunawa tare da yauƙaƙa danƙon abota a tsakanin ‘yan wasan, tare da yin amfani da wannan dama wajen sanar da ‘yan Nijeriya cewa harkokin tsaro sun inganta a jihar Yobe.
Geidam ya ce ƙungiyoyi biyar ne suka fafata a gasar, waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi biyar tsakanin Yobe da Borno.
