Sarkin Gusau ya ƙaddamar da rigakafin shan’inna na Yuni

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mai martaba sarkin Katsinan Gusau Alh. Ibrahim Bello a Jihar Zamfara ya ƙaddamar da shirin rigakafin cutar shan inna na watan Yuni watau (OBR) wanda hukumar UNICEF da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar ta shirya aiwatarwa a faɗin jihar.

Basaraken ya bayyana haɗin gwiwa da hukumar UNICEF ta yi a jihar don inganta lafiyar yara ƙanana a matsayin abin farin ciki da samun ci gaba, inda ya ce masarautar tasa za ta cigaba da bada duk wani tallafi da ya dace don ganin an samu nasarar gudanar da rigakafin.

Alh. Ibrahim Bello ya ƙara jaddada buƙatar sake fasalin gudanar da rikagafin da hukumar UNICEF takeyi da nufin isa ga dukkan lungu da saƙo na jihar.

A cewarsa, ya kamata hukumar ta UNICEF ta ƙara ba da tallafi musamman kayan abinci ga iyaye domin ƙarfafa musu gwiwa wajen fitar da ‘ya’yansu ‘yan ƙasa da shekara biyar a yi musu rigakafi a lokacin.

“Ya kamata hukumar UNICEF ta faɗaɗa abin da zai ƙarfafa gwiwar iyaye da wani abu musamman ta hanyar samar wa iyaye wasu nau’ikan abinci iri-iri a yayin gudanar da rigakafin maimakon raba kayan zaƙi ga yara duba da irin halin ƙuncin da ake ciki na tattalin arziki wanda hakan zai shawo kan iyaye su aminta a yiwa ‘ya’yansu allurar”. Sarkin ya bayyana

Ya buƙaci iyaye da su ƙara ƙaimi domin tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun samu rigakafin cutar shan inna a jihar.

A nasa jawabin, ƙwararre kan manufofin zamantakewar al’umma, kuma jami’in kula na UNICEF, ofishin dake Sokoto, Isah Ibrahim, ya ce domin daƙile cutar shan inna, kashi 95 cikin 100 na yara ‘yan kasa da shekaru biyar suna buƙatar allurar rigakafin cutar shan inna ta baka aƙalla sau uku a jere.

Ya kuma ƙara da cewa, bisa la’akari da ƙididdigar yawan jama’a da kiwon lafiya na shekarar 2023 (DHS), Penta uku na jihar Zamfara ya kai kashi 25 cikin 100, kuma daga cikin ƙananan hukumomi 14 na jihar, ƙananan hukumomin jihar guda 6 (Gummi, Gusau, Bungudu, Maru, Ƙaura Namoda, da Talata Mafara) na cikin kashi 100 na ƙananan yara na Najeriya.

Yace ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da UNICEF ke fuskanta shi ne, rashin sani muhimmancin rigakafin da rashin fahimta da kuma haifar da rashin bin allurar rigakafin cutar shan inna a jihar.

“Dole ne mu yarda cewa akwai manyan ƙalubale, muna neman kulawar gaggawa da mai da hankali don tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba.

“Muna kira gare ku da ku nemi sahihin bayanai daga amintattun ƙwararrun masana kiwon lafiya da shugabannin al’umma, rawar da kuke takawa wajen kare lafiyar ‘ya’yanku abu ne mai kima, kuma ta hanyar yi wa yaranku alluran rigakafi, kuna bada gudummawa ga cigaban al’ummarmu”. Isah Ibrahim yace

By ukarofi