Sarkin Gusau ya yaba wa al’ummar Ibo kan cigaban kasuwanci

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sabon Sarkin Gusau a Jihar Zamfara, Mai Martaba Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, ya yabawa al’ummar Igbo mazauna masarautar sa bisa jajircewar da suke yi na bunƙasa harkokin kasuwanci a Jihar Zamfara, musamman Gusau babban birnin jihar.

Sarkin ya yi yabon ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin mambobin ƙungiyar Eze Igbo na Gusau, ƙarƙashin jagorancin Cif Egbuna Obijiaku, da shugabannin kungiyar ‘yan ƙabilar Igbo (ICA), waɗanda suka kai masa ziyarar taya murna da naɗin da aka yi masa a matsayin Sarkin Gusau na 16 da kuma ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Marigayi Sarki Ibrahim Bello wanda ya rasu kwanakin baya.

Sarkin ya ƙara da cewa ‘yan ƙabilar Igbo na da karfi a Masarautar, inda ya ce sun bayar da gudunmawa sosai wajen haɓaka tattalin arzikin jihar.

“Naji daɗin ziyarar da kuka kawo min domin ta’aziyya game da rasuwar mahaifina, Marigayi Sarki tare da jin daɗin yadda kuke bayar da gudunmawa wajen haɓaka tattalin arziki da cigaba a fannin kasuwanci musamman ƙanana da matsakaitan masana’antu a masarautata”. Yace

Da yake mayar da martani, Eze Igbo na Gusau da shugaban ICA a Zamfara, Nnamdi Ageramu, sunce sun kasance a fadar sabon sarkin ne domin jajanta masa bisa rasuwar mahaifinsa, tare da bayyana cewa za su cigaba da biyayya ga masarautar a koda yaushe.

Sun bayyana marigayi Sarki Ibrahim Bello a matsayin uba ga ƙabilar Ibo, mai samar da zaman lafiya wanda ke kare martabar kowace ƙabilar da ke zaune a masarautarsa idan buƙatar hakan ta taso a lokacin rayuwar sa.

“Marigayi Sarkin mahaifinmu ne, wanda ya kula da jama’arsa da gaske ba tare da la’akari da banbancin ƙabila ba, kuma muna so my tabbatar muka da cewa al’ummar Ibo na da aminci kuma za su cigaba da biyayya ga masarautar ka.” Inji shi.

By ukarofi