Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen Malamin addinin Musulunci nan, Malam Kabiru Ibrahim Na Madabo.
An yi Jana’izar ne da ƙarfe 10 na safiyar yau Juma’a a filin Ƙofar Kudu da ke masarautar Kano.
Shahararren malamin ya rasu ne a jiya Alhamis, bayan sallar La’asar a gidan sa da ke ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano.
Ɗimbin al’ummar musulmi ne suka halaccin janaizar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
