Sarkin Kasuwar ƙofar Wambai ya naɗa Ibrahim ɗan Amana sarautar Magajin Garin kasuwar

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Sarkin Kasuwar ƙofar Wambai, Alhaji Bashir Adamu ya naɗa Alhaji Ibrahim Lawan ɗan Amana, sarautar Magajin Garin Kasuwar ƙofar Wambai .

Taron naɗin wanda ya gudana a ƙarƙashin jagorancin majalisar Sarkin Kasuwar ƙofar Wambai ranar Laraba ya samu halartar ‘yan kasuwa daban-daban.

A jawabinsa ga manema labarai bayan naɗa shi Magajin Garin kasuwar ƙofar Wambai Alhaji Ibrahim ɗan Amana ya yi godiya ga masarautar Kano ƙarƙashin Khalifa Muhammad Sanusi da  wakilin Gabas da Sarkin Kasuwar ƙofar Wambai bisa wannan sarauta da  suka sahale aka yi masa naɗin.

Ya nuna gamsuwa da irin ayyukan da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yake na cigaban al’ummar Kano kuma  za suyi amfani da wannan naɗin da aka yi masa wajen cigaba da tallafawa bunƙasa haɗin kai da cigaban ‘yan kasuwar ƙofar Wambai.

Alhaji Ibrahim Lawan Ayagi ɗan Amana ya gode wa ɗimbin ‘yan kasuwa da ƙungiyoyi daban-daban da sauran mutane da suka nuna masa ƙauna suka zo suka shaidi naɗin nasa da kuma taya shi murna akai.

Shi ma shugaban, shugabannin ƙungiyoyin kasuwar ƙofar Wambai gabaɗaya wanda kuma shine  mataimakin shugaban ƙungiyar ‘yan koli na kasuwar ɗan majalisar masarautar Sarkin kasuwar ƙofar Wambai, Alhaji Shariff Nata’ala Isma’il ya ce ba su yi mamakin naɗin da aka yi wa ɗan Amana sarautar ba.

Ya ce ganin irin tsare-tsaren da masarautar take da shi na wakilai da suke kula da dukkan wasu al’umma da suke a cikin kasuwar tasa aka yi wannan naɗin  wanda ƙoƙari  ne na ta ga ta sauke nauyin amanar da Allah ya ɗora mata.

Sharu Nata’ala Isma’il ya ce yanzu saboda tsari da suke da shi a masarautar kasuwar ƙofar Wambai kafin aga sun fita da wani al’amari waje na matsala da ya shafi tsakanin ‘yan kasuwa zuwa wajen jami’an ‘yan sanda ko alƙali yana da wuya saboda yadda masarautar ta baza wakilai saƙo-saƙo ake daidaita tsakani da yin sulhu idan wani abu ya taso.

Alhaji Sharu Nata’ala Isma’il ya  shawarci sabon magajin garin kasuwar ƙofar Wanbai Ibrahim ɗan Amana akan nauyi da amanar da aka ɗora masa ya yi aiki bisa  gaskiya da riƙon amana kamar yanda dama jama’a suka shaide  shi akai. Su kuma al’umma su ba shi haɗin kai domin cimma nasara.

Ita ma a nata ɓangaren mai ɗakin sabon magajin garin kasuwar ƙofar Wambai, Hajiya Maryam  Lawan ɗalladi ta bayyana mutuƙar farin cikinta bisa zaɓo mai gidanta da akayi a cikin dubbai aka bashi wannan matsayi suna yiwa Allah godiya  bisa wannan tare da masoya  shi kuma tayi addu’ar Allah ya bashi  ikon sauke  nauyi da aka ɗora masa.

Ta ƙara da cewa ba ta yi mamakin irin ɗinbin mutane da suka halarci bikin naɗin ba, domin ta  san mijinta mutum ne na mutane mai halaye masu kyau  da  yake da kyakkyawan mu’amala sa jama’a shi ya sa suka  taru.

Hajiya Maryam Lawan ɗalladi ta jaddada  yiwa mai gidan nata Alhaji Ibrahim Lawan ɗan Amana magajin garin kasuwar ƙofar wanbai addu’a da fatan sauke nauyi da  Allah ya bashi.

Shi ma ɗaya daga cikin yan’uwan  sabon magajin garin kasuwar ƙofar wanban.Alhaji Falalu ya ce  wannan rana ce ta farin ciki ga yan kolin jihar Kano gaba ɗaya ba kawai na kasuwar ƙofar  Wanbai ba suna da kyakkyawan zato akan  wanda aka yiwa wannan naɗin  domin mutum ne  mai kyakkyawan mu’amala da haƙuri.

Alhaji Falalu Lawan Ayagi ya ce babban farin cikinsu game da ɗan Amana mutumin kiki ne su da suke ‘yan uwansa kullum jin daɗinsa suke kuma kowa sai sanyawa naɗin nasa albarka yake. 

By ukarofi