Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar kula da rajistan ababen hawa DRTS da Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) sun markaɗe babura 601 da suka kama suna aiki a garin.
Sakataren fannin sufuri na FCTA Elechi Chinedum ya sanar da haka ranar Talata.
Chinedum ya ce hukumomin sun kama waɗannan babura ne bisa ga laifin amfani da su a wuraren da aka hana amfani da su a Abuja.
Ya ce tsarin dokan ya kuma bai wa mahukuntan Abuja ikon kamawa tare da markaɗe duk babur ɗin da ya saɓa wa tsarin dokar.
Chinedum ya yi kira ga ‘yan achaɓa da su daina haya da baburansu a wuraren da gwamnati ta hana amfani da su a Abuja cewa idan har suka kama sun rasa su kenan.
Bayan haka shugaban Hukumar DRTS Abdulateef Bello shima ya yi kira ga waɗanda ke da hannun jari a sana’ar achaɓa da su sake shawara cewa Hukumar za ta ci gaba da amfani da ikon da dokar ta ba su na kama duk baburan da suka saɓa wa doka.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na Abuja Mode Magawata ya ce Ministan Abuja Nyesom Wike ya Hana amfani da babura a wasu ɓangarorin Abuja domin hana muggan ayyuka a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Magawata ya tabbatar cewa rundunar za ta ci gaba da mara wa mahukuntan Abuja domin ganin sun ci gaba da zartar da wannan doka domin samar da tsaro a Abuja.
