Fadar Shugaban ƙasa za ta binciki manyan makarantu 51 kan lamunin NELFUND na ɗalibai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani martani mai ƙarfi ya biyo bayan zargin cewa aƙalla manyan makarantu 51 ne ke da hannu wajen cire kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, da karɓar kuɗaɗe biyu na hukumomi daga cibiyoyin da za su amfana, da kuma cin gajiyar shirin lamunin ilimi na Nijeriya (NELFUND).

A zantawarsa da jaridar nan da safiyar Laraba a Abuja, babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin ɗalibai, Sunday Asefon, ya yi Allah-wadai da shugabannin manyan makarantun da suke aikata laifukan cirewa da karɓar kuɗaɗe biyu daga ɗaliban da ke cin gajiyar shirin NELFUND.

Asefon, tsohon shugaban ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS), ya bayyana cewa zai yi hulɗa da ƙungiyoyin ɗalibai na jami’o’i, kwalejin kimiyya da fasaha, da kwalejojin ilimi, sannan kuma su tattauna da ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa.

Mai taimakawa shugaban ƙasar ya yi kira da a kafa kwamitin sa ido wanda ya ƙunshi ɗalibai da za su sanya ido kan yadda ake biyan kuɗaɗen a shiyyoyin siyasar ƙasar nan shida.

Kalamansa: “Dole ne in yi Allah wadai da mataimakan shugabannin jami’o’in da suka samu biyan kuɗin lamunin ɗalibai, kuma suka kasa sanar da ɗalibai, suka ci gaba da karɓar kuɗin makaranta daga hannun waɗannan ɗaliban.

“Wasu ma har sun hana ɗalibai rubuta jarrabawa bayan sun karɓi kuɗaɗen daga NELFUND.

“Ina yin Allah wadai da shi gaba daya kuma yayin da nake magana da ku, ofishina, shugabannin ɗalibai a faɗin ƙasar nan da suka haɗa da NANS, ƙungiyar ɗaliban jami’o’i ta ƙasa (NAUS), ƙungiyar ɗaliban kwalejin ilimi ta ƙasa, ƙungiyar ɗaliban Polytechnic ta ƙasa (NAPS), muna taro kuma muna aiki don ganawa da Ministan Ilimi, kuma muna da kwamitin da zai sanya ido a duk yankuna shida na ƙasar nan. Da zaran an sanar da NELFUND za a iya rabawa ɗalibai.

“Kafin shugabannin jami’o’i su rubuta wa NELFUND don samun sanarwar, da ɗaliban sun sanar da abokan aikin su cewa NELFUND ta fitar da wannan adadin.”

Ya bayyana damuwarsa cewa shugabannin hukumomin da galibinsu suka ci gajiyar ilimi kyauta a zamaninsu, su ne ke ƙoƙarin kawo cikas ga manufofin Shugaba Bola Tinubu na rancen ɗalibai.

“Ina mai tabbatar muku, nan ba da jimawa ba za mu bayyana sunayensu, kuma duk makarantar da aka samu tana irin wannan aika-aika, ɗaliban Nijeriya ba za su samu sauƙi ba.

“Kun san ‘yan Nijeriya, mu ne matsalar da kanmu. Ka yi tunanin shugaban ƙasa wanda ke da wannan hangen nesa, wanda ya yi imanin cewa ba da ilimi shine kawai don ba da rai. Kuma ga waɗanda iyayensu ba su da ikon tura ‘ya’yansu makaranta, kuma shugaban ya ji cewa akwai buƙatar kowane gida ya samu ingantaccen ilimi,” inji shi.

Da take mayar da martani kan zargin, Kwalejin Fasaha ta Yaba (YABATECH) ta bayyana hakan a matsayin ba gaskiya ba ne, inda ta dage cewa kuɗaɗen da ake zargin an biya kwalejin na ƙarƙashin CBN ne ta tantance su.

Kakakin makarantar, Adams Adekunle, ya yi kira ga ɗaliban da su yi haƙuri, domin za a biya su a kan lokaci.

A cewarsa, “Dole ne a bi ƙa’idoji da tsare-tsare na lissafin kuɗi a duk wata hada-hadar kuɗi, adadin kuɗin da ake zargin an biya Kwalejin yana ƙarƙashin CBN ne ta tantance shi.

“Kuɗaɗen da aka kafa kamar yadda aka ce an biya har yanzu ba a nuna su a cikin asusun Kwalejin ba.”

A halin yanzu, NELFUND ta dage cewa “ba a tuntube ta don wannan rahoto ba kuma ba ta bayar da wani bayani, sharhi, ko gudummawa ga wallafawa ba.”

Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Manajan Daraktan NELFUND, Akintunde Sawyerr, ta ce asusun ba tare da wata shakka ba ya raba kan sa daga labarin.

By ukarofi