Zamfara: Shugaban NYSC ya buƙaci ’yan hidimar ƙasa su mutunta al’adun al’umma

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD anusi a Gusau

Babban Darakta Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) Birgediya Janar OO Nafiu, ya buƙaci  ‘yan bautar ƙasa da aka tura jihar Zamfara da su mutunta al’adu da kimar al’ummar da suka karɓi baƙuncinsu. 

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi ga 2025 Batch “A” Stream I Corps Members a NYSC Orientation Camp, Gusau, Jihar Zamfara ranar Laraba. 

A cewar shugaban masu yi wa ƙasa hidima na NYSC, babban maƙasudin shirin shi ne inganta dunƙulewar ƙasa da haɗin kan ƙasa, don haka ya buƙaci ‘yan ƙungiyar da su yi amfani da damar su wajen yi wa ƙasa hidima domin koyon yare da kuma bunƙasa ilimin jihar. 

Shugaban hukumar ya tabbatar wa da ‘yan ƙungiyar cewa tsaron lafiyar su shi ne babban fifiko kuma ba za a tura su wuraren da ba a yi cikakken tantancewar tsaro ba.

Janar Nafiu, ya shawarci ‘yan ƙungiyar da su riƙa karanta duk wasu shawarwarin tsaro, su samu izini hukuma kafin tafiya, baya ga gujewa tafiye-tafiyen dare. 

A cikin kalamansa, “Na zo nan ne domin in ba ku ƙwarin gwiwar cewa NYSC ta shafi haɗa kan ƙasa baki ɗaya, da ci gaban ƙasa da kuma gina ƙungiyar matasa masu nagarta da za su samu nasarar karbar ragamar shugabancin kasar nan da kuma inganta ta nan gaba kaɗan. 

“Na yi imanin cewa don kun zo wannan mataki, kuna da duk abin da kuke bukata don samun nasara a rayuwa kuma kuna da duk abin da kuke bukata don ɗaukar nauyin jagoranci, ku yi wa iyayenku da al’umma alfahari.

Ina ba ku shawarar ku zauna lafiya da kowa, kada ku matsa wa kanku don sake aiki. Ku zauna a nan, ku ji dadin Jihar Zamfara, ku koyi harshen su kuma ku sami karin fasaha. 

Birgediya Janar Nafiu ya kara da karfafa gwiwar ‘yan bautawa kasar da su dauki shekarar hidimarsu da muhimmanci tare da yin amfani da shirin Koyarwa da bunkasa kasuwanci (SAED) yadda ya kamata. 

A jawabin maraba, Kodinetan NYSC na jihar Zamfara, Mallam Muhammad Lawan Ahmed ya yabawa shugaban hukumar bisa wannan ziyarar, inda ya bayyana cewa ‘yan kungiyar sun saba da sabon yanayin da suke ciki, kuma suna karbar horon da ya dace ga duk wani horo na sansani. 

Ya bayyana cewa jihar ta ci gaba da haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da ingantaccen tsaro da walwalar ‘yan ƙungiyar a jihar. 

By ukarofi