Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu
Gwamnonin Arewa maso Gabas sun fara taron ƙungiyar gwamnonin, a karo na 11, wanda aka fara da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Alhamis, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Taron ya samu halartar gwamnonin yankin; Gwamnan Adamawa, Borno, Bauchi, Taraba, Gombe da Yobe, mai masaukin baƙi.
Sa’ilin da yake jawabi kan taron, shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin, kuma Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jaddada buƙatar ɗaukin gaggawa wajen magance matsalolin da yankin yake fuskanta, musamman a fannonin karancin abinci, tabarbarewar harkokin sufuri, kiwon lafiya, sannan uwa uba, koma bayan tattalin arziki.
Gwamnan Zulum ya yi tsokaci dangane da yadda taɓarɓarewar harkokin tsaro ke ci gaba da zafafa a yankin, yayin da kuma ya yaba wa kokarin sojojin Nijeriya, ta fuskacin yaƙi da matsalolin tsaron, ind ya ce, “Ina kira gareku, ku ci gaba da yaki da yan ta’adda har sai mun kawo karshen wannan matsalar.
“Dawowar hare-haren yan ta’adda a cikin jihohinmu wani al’amari ne mai matukar tayar da hankali wanda hakan zai iya kara ta’azzara nasarorin da aka samu a fagen yaki da matsalolin tsaro. Ina mai bayar da shawarar cewa sojojinmu su fadada sabbin dabarun da suke dasu wajen dakile farmakin yan ta’adda.”
Gwamna Zulum ya ce, “ƙangin talaucin da yankinmu yake fuskanta, abin tsoro ne, kuma ya zama dole mu dauki ingantattun matakai don magance wannan kalubale. Mu fahimci cewa talauci babbar barazana ne ga tattalin arziki, wanda zai iya shafi zamantakewa.”
“A kokarin nemo madafa, noma kaɗai ba zai kasance mafita ba, a yaki da talauci. Dole mu kara mayar da hankali kan samar da kyakkyawan yanayi don kafa kananan da matsakaitan masana’antu a yankin mu.”
“Abin ya hada da sa hannun jari a kayayyakin more rayuwa, bayar da fifiko wajen zuba jari mai yawa ga kamfanoni masu zaman kansu, don habaka kasuwanci da kirkire-kirkire.”
Ya ce dole ne su yi aiki don rage talauci ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa tunani tare da tallafa wa kananan masana’amtu, bunkasa kasuwanci, ta fuskar habaka masana’antu, don fadada tattalin arziki tare da samar da dama ga matasa.
Da farko, mai masaukin bakin taron, kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a lokacin da yake jawabin bude taron, ya ce a matsayinsu na Gwamnonin yankin za su yi amfani da dandamalin wajen yanke shawarar da za ta kai ga samar da mafita ga matsalolin da yankin yake fuskanta.
“Irin karfin niyya da kyakkyawan kudurori, shawara mai nagarta, da daukakar mataki a cikin gaggawa, wanda shugabanin mu da suka gabata, ko shakka babu sun haskaka makomar yankin Arewa maso Gabas.
“Yau ma gashi mun taru domin daukar sabbin kudurori da shawarwari nagari, don bin sawun magabatanmu wajen kawo ci gaba a yankinmu.”
