Ranar Ma’aikata: Har yanzu akwai masu albashin da bai kai N30,000 ba a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Ranar ɗaya ga watan Mayu ita ce aka yi ittifaƙi a matsayin Ranar Ma’aikata ta Duniya, inda ma’aikata ke haɗuwa a wani dandali tare da shugabanni don gabatar da jawabai yayin da su kuma shugabannin ƙungiyoyin ma’aikatan ke gabatar da ƙorafe-ƙorafen su a madadin sauran ma’aikata.

Jihar Kebbi ita ma ta bi sawun sauran sassan jihohin Nijeriya kamar yadda aka saba a dandalin filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin Kebbi.

Sai dai wannan bikin na ranar ma’aikatan na bana bai yi wa ma’aikatan jihar Kebbi daɗi ba musamman malaman firamare da ke fama da matsalolin albashin da bai taka kara ya karya ba.

A tunaninsu zai yi maganar aiwatar da tsarin albashi na dubu saba’in a mafi ƙarancin albashi amma sai dai bai taɓo wannan maganar ba a maimakon haka ya bai wa maganar komawa sabuwar sakateriya da aka gina nan ba daɗewa ba.

Wani malamin firamare da ya zanta da wakilinmu ya nuna rashin jin daɗinsa bisa ga yadda gwamnatin jihar Kebbi ta mayar da malaman firamare saniyar ware a cikin tsarin ma’aikatan gwamanti duk da kasancewar malamai su ne tushen duk wani ilmi, bayan wannan kuma babban abin ban haushi shi ne, shi maigirma gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya daga cikinsu wanda a duk matsayin da kai bai wuce darajar malami ba saboda wannan matsayin daya ke a yanzu na gwamna ai ya samo asali ne daga shugabancin kungiyar malamai ta (NUT) wanda ya soma tun daga matakin karamar hukuma zuwa jiha har Allah ya kai shi ga shugabancin kungiyar na kasa bakiɗaya. 

“Wannan gaskiya abin ban haushi ne a ce irin Malam Nasir Idris yana gwamna amma malamai kuma suna tagayyara a jiharsa,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “yanzu haka akwai malamai a jihar Kebbi da ke karɓar albashin da bai kai naira dubu talatin ba duk da gyare-gyaren da ya ce ya yi na matakan aiki.”

Ya yi kira ga gwamnan da ya nemi hanyar gyara albashin malamai saboda kaucewa ajiye aiki tunda yanzu malamai sun gano idan malami ya dade yana aiki amma ana biyan sa albashin da bai taka kara ya karya ba amma idan ya ajiye aiki sai ka ga fansho din sa yana iya ninka albashin da ake ba shi sau kusan hudu.

Wannan ya sanya malamai da yawa suna da kudurin ajiye aiki saboda kawai su samu wannan fansho mai yawa kuma ba tare da suna wani aiki ba.

By ukarofi