Sarkin Katsina ya taya Sunusi Saulawa murnar zama muƙaddashin provost marshal a hukumar Kwastom

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ta taya Tasi’u Sanusi Saulawa zama muƙaddashin Provost Marshal na hukumar Kwastam ta Najeriya.

A wata sanarwa, Sarkin ya bayyana cewa naɗin Saulawa ya zo ne bisa cancanta da ƙwarewa, tare da nuna jin daɗinsa da alfahari ga wannan matsayi da ɗan asalin Jihar Katsina ya samu.

Mai Martaba ya ƙara da cewa wannan naɗi babban nauyi ne da ke buƙatar jajircewa, riƙon amana da kuma aiki tuƙuru domin tabbatar da an cika amanar da aka ɗora masa.

Sarkin Katsina ya yi addu’ar Allah ya ba Saulawa lafiya, hikima da nasara wajen gudanar da wannan sabon aiki, tare da fatan zai ci gaba da kawo ci gaba ga ƙasa da al’umma baki ɗaya.

Haka kuma, ya bayyana cewa wannan nasara abin alfahari ne ga masarautar Katsina da ma Jihar baki ɗaya, yana mai fatan za ta ƙara inganta suna da martabar jihar a matakin ƙasa.

Ya yi fatan Allah ya ƙara masa ɗaukaka tare da ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa.

By ukarofi