Sarkin Rano yana bada kulawa sosai wajen kare kimar al’adun mu – Uban Doman Rano

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa Sarkin Rano, Alhaji Kabiru Autan Bawo da cewa yana kan gaba wajen himmatuwa da bada kulawa wajen ɗabbaƙa raya al’adun mu na gargajiya.

Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sanda mai kula da sashen sufuri, Yusuf Usman Chiromawa. Uban Doman Rano. Walin Garun Malam shine ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ce koda shiga ta Ado da Autan Bawo Sarkin Rano yake a koyaushe yana wakiltar suturar al’dummu na gargajiya ne, duk wani abu na cigaba yana ƙoƙari ya ga ya tafi da tsari na al’adarmu don kiyaye kimar mu da ɗorewar tarihi, koyaushe sarki na kishinsa ga bunƙasa al’adu.

Ya ce abu ne mai muhimmanci ace an bai wa masu sarautun gargajiya dama a tsarin mulki da za su riƙa yin aiki na kyautata rayuwa da zamantakewar al’umma ba wai sai wata rigima ta taso ba ko ana son cimma wata buƙata ba sannan a yi kiransu.

Ya ce rabuwa da su da aka yi shi ya sa aka samu vullar abubuwa marasa daɗi a wasu sassa na jihohin ƙasar nan sake kawo rashin kwanciyar hankali amma idan aka ce ƙananan hukumomi suna aiki yadda yakamata sarakuna suna aiki to za a sami tsaro domin za su sa ido duk wanda zai zo an san shi a gane na ƙwarai ne ko ba na kwarai ba ne a yi maganin abin run daga tushe.

Mataimakin Sufeton na ‘yan sanda ya yi jan hankali ga matasa akan su dagewa neman ilimi duk da cewa a yanayin halin da ake ciki na ta’azzarar matsin tattalin arziƙi su daure da yardar Allah in suka yi ilimi ba za su yi da na sani ba a rayuwar su.

Sannan ya gargaɗi matasa akan su guji jefa kansu akan shan miyagun ƙwayoyi sannan su kuma iyaye su zama masu kula da sanya ido kan tarbiyar ‘ya’yansu ta yadda za su zama masu amfani ga al’umma.

Uban Doman na Rano, Alhaji Yusuf Usman ya yi kira ga al’umma su guji ‘yan siyasa su ruƙa raba kansu saboda bambamcin siyasa domin su manyan kawunansu a haɗe yake amma suna raba kawukan talakawa don cimma manufarsu.

Uban Doman Rano, Walin Garun Malam, Yusuf Usman Chiromawa ya ce a tsari na dimukraɗiyya ikon juya mulki na hannun al’umma ne don haka duk wanda bai yi daidai ba suna da dama su sauya shi lokacin zave don haka kar su yarda azo musu da vangaranci ko maganar bambancin addini ko yare don a raba kai. A kula da wanda zai kawo haɗin kan ƙasa da zai amfani ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *