Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti zai karɓi ragamar horar da Tawagar Ƙwallon Ƙafar Brazil a kaka mai zuwa kamar yadda shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar, Ednaldo Rodrigues ya bayyana.
Brazil wadda ta lashe kofin duniya har sau biyar, na da kwarin guiwar cewa, Ancelotti, shi ne zai jagoranci ƙasar zuwa gasar Copa America da za ta gudana a cikin watan Yunin 2024.
Brazil ba ta da wani tsayayyen koci tun lokacin da aka kammala gasar kofin duniya a bara, bayan da kocinta Tite ya yi murabus jim kaɗan da aka lallasa a hannun Croatia.
Ancelotti zai kafa tarihin zama wani koci daga ƙetare da Brazil ta ɗauko tun daga shekarar 1965.
Kodayake kawo yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Ancelotti ko Real Madrid kan cewa, kocin zai raba gari da ƙungiyar nan da shekara mai zuwa domin komawa Brazil da aikin horarwa.