Daga AMINA YUSUF ALI
Bankin FirstBank na Nijeriya ya ƙaddamar da wani mutum-mutumin ma’aikacin banki a reshensa na Adetokunbo Ademola VI, (DXC) a Legas don kula da koken masu ajiyar bankin.
Folake Ani-Mumuney, Shugaban rukunin bankuna, da kasuwanci da hulɗar kamfanoni na FirstBank, shi ya bayyana haka a cikin wani jawabi da gabatar a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata.
A cikin jawabin nasa ya bayyana cewa, mutum-mutumin yana da girkakkiyar kyamara ta bidiyo da fasahar na’ura mai ƙwaƙwalwa wanda zai mayar da shi tamkar ɗaya daga cikin ma’aikata masu fara’a na reshen bankin.
Wannan wani yunquri ne irinsa na farko da bankin ya yi na ganin an havaka harkar banki a Nijeriya.
Kuma a cewar sa, wannan mutum-mutumin yana ɗauke da bidiyo na harkar banki da fasahar zamani, kuma yana mu’amala da masu ajiyar ta hanyar yin hira da su da kuma sikirin na tavawa da yake ɗamfare a kan ƙirjinsa.
Ayyukan da zai dinga yi sun haɗa da warware matsalolin masu ajiya da suka shafi ajiyar kuɗi, fitar da kuɗi, da matsalar katinan ATM.
Haka yana iya taimakawa wajen gudanar kula da ƙorafe-ƙorafen mutane a bankin. Sannan yana tallata sababbin abubuwan da suka shafi bankin ga mutane da gamsar da masu ajiya.
A taqaice ma dai yakan ilimtar da mutane a game da tsare-tsaren bankin. Sannan ya lura da asusun mutane yadda ya kamata.
A taƙaice dai wannan sabuwar fasahar mutum-mutumin an samar da ita saboda ƙara kyautatta wa masu ajiya da kuma inganta rayuwarsu ta harkar bankin. Inji Adesola Adeduntan, Babban jami’in zartarwa na Bankin FirstBank.
Kuma a cewar sa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba don ganin sun kawo abinda zai kyautatta rayuwar masu ajiyarsu ba. Kuma a cewar sa ana sa ran samar da wani mutum-mutumin a bankin na First bank nan da wata guda.