Amarya ta yi ajalin angonta a Bauchi

Wata amarya mai suna Maimuna Suleiman ‘yar shekaru 21, ta kashe mijinta Aliyu Muhammad ta hanyar daɓa masa wuƙa a unguwar Ƙofar Ɗumi dake Bauchi.

‘Yan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar hakan tare da cewa, suna tsare da amaryar don zurfafa bincike.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na Bauchi, ASP Aminu Gimba Ahmed ya ce lamarin ya faru ne ranar 5 ga Yulin 2023 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

Ya ƙara da cewa, bayan da suka samu labari sun garzaya gidan inda suka ɗauki mijin da matar zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ABUTH).

Ya ce likitoci sun bincika kuma sun tabbatar mamacin ya rasu ne sakamakon raunin da ya samu a ƙirjinsa, yayin da wacce ake zargin ta samu ƙananan raunuka a cikinta.

Kakakin ‘yan sandan ya ce wadda ake zargi ta amsa laifinta.

A yanzu haka dai sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda na ci gaba da bincike kafin gurfanar da ita gaban kotu.