Saudiyya ta haramta shan barasa a Gasar Kofin Duniya na 2034

Daga BELLO A. BABAJI

Jakadan Saudiyya ga Birtaniya ya ce ba za a amince da shan giya a lokacin gasar kofin duniya na shekarar 2034 da ƙasar za ta jagoranta ba.

A wata hira da LBC ta yi da shi, Khalid bin Badar Al Saud ya ce ba za a sayar da barasa a ko’ina a ƙasar ba a yayin gudanar da gasar ciki har da otal-otal.

Ya kuma ce za a iya samun nishaɗi ta hanyoyi da dama, ya na mai cewa haka al’adarsu ta ke, don haka ba za su canza ta ba saboda buƙatar wasu.

Hakan na zuwa ne a lokacin da batun sayen barasa ya zama abin tattaunawa musamman a lokacin da aka gudanar gasar a Qatar, a 2022 inda aka samu tsauraran matakai na sayar da giya.

Haka kuma batun auren jinsi da sauya jinsi zuwa mata-maza, waɗanda suma haramun ne a Saudiyya ba za a karɓe su ba, ta na mai cewa za su marabci kowaye koma-bayan masu irin waɗanda ɗabi’un.

Ana zargin ƙasar da sauya tunanin al’umma ta hanyar kashe kuɗaɗe masu yawa a wasanni wanda hakan yana tasiri ga martabarta a idon duniya.

Kungiyar fafutukar ƴancin ɗan-adam ta ‘amnesty international’ ta ce gudanar da gasar a ƙasar ka iya haifar da tsawwalawa da tauye haƙƙin al’umma.