Saudiyya ta sako ’yan Nijeriya da aka maƙala wa ƙwayoyi a jaka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar da sakin ’yan Nijeriya uku da aka tsare a ƙasar Saudiyya bayan da aka kama su a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah a watan Agustan 2025 bisa zargin shigo da haramtattun abubuwa.

Sanarwar ta fito ne a wani saƙo da Fadar Shugaban ƙasa ta wallafa a shafinta na ɗ a ranar Alhamis.

Waɗanda aka saki sun haɗa da Sadiya AbdulHamid, Hajiya Maryam Hussein Abdullahi da kuma Hajiya Bahijah Aminu Abdullahi.

Bayanin ya nuna cewa an kama su ne bayan gano wasu haramtattun abubuwa a cikin kayan da suka tafi da su, waɗanda wasu gungun masu laifi suka maƙala musu a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) ba tare da saninsu ba, ta hanyar damfarar tikitinsu.

Tun da aka samu labarin afuwar, Jakadan Nijeriya a Jeddah, Ambasada Mu’azam I. J. Nayaya, ya hanzarta tuntuɓar hukumomin Saudiya, ya sanar da Ma’aikatar Harkokin Waje a Abuja tare da neman haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Safarar Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA domin gudanar da cikakken bincike.

Ofishin jakadancin Nijeriya ya ci gaba da zama cikin mu’amala da hukumomin Saudiya, tare da ziyartar waɗanda aka tsare akai-akai da kuma samar musu da lauyoyi da za su tsaya musu a gaban kotu.

Bayan kammala bincike mai zurfi, hukumomin Saudiyya sun wanke ’yan Nijeriyan uku daga dukkan zarge-zarge tare da tabbatar da rashin hannu nasu a laifin da ake tuhumarsu da shi.

A cewar sanarwar, Hajiya Maryam Hussein Abdullahi da Hajiya Bahijah Aminu Abdullahi sun koma Nijeriya tun a ranar 5 ga Nuwamban 2025, yayin da aka ɗage dokar hana tafiye-tafiye da aka ƙaƙabawa Sadiya AbdulHamid a ranar 2 ga Nuwamban 2025, inda ake shirin dawo da ita gida nan kusa.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta yaba da yadda hukumomin Saudiyya suka nuna kwarewa da adalci a wannan lamari, tare da yabon rawar gani da NDLEA da kuma ofishin jakadancin Nijeriya a Jeddah suka taka wajen tabbatar da samun sakamako na adalci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan nasara na nuna jajircewar gwamnatin Nijeriya wajen kare rayuka da martabar ’yan ƙasarta da ke ƙasashen waje, daidai da manufar “4D Doctrine” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

By ukarofi