Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Masarautar AlUla a ranar Larabar da ta gabata ta ce lardin AlUla na ƙasar Saudiyya ya kafa kansa a matsayin fitaccen wurin noma, inda yake samar da sama da tan 1,000 na mangwaro a duk shekara.
Hukumar ta ce, AlUla na da itatuwa sama da 50,000 da aka dasa a faɗin yankin.
Ya ce gonakin mangwaro da ke lardin ya kai kusan hekta 125 kuma ana samar da kusan tan 1,125 na nau’in mangwaro daban-daban a duk shekara, wanda hakan ya sanya AlUla a cikin yankunan da ke kan gaba wajen noma a masarautar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ruwaito haka, inda ya naƙalto wasu alƙaluma daga hukumar masarautar AlUla.
Shahararrun nau’ikan mangwaro na gida sun haɗa da “Zebda”, “Senara” da “Keitt”, waɗanda aka sani da inganci da ɗanɗano na musamman, waɗanda ke nuna ƙasa mai albarka da yanayi mai kyau na yankin.
Lokacin girbin mangwaro a AlUla yana farawa daga watan Yuli zuwa watan Satumba, wanda hakan ya sa ya zama wuri mai ban sha’awa ga masu son ‘ya’yan itacen da kuma masu ziyartar gonakin gida. Hukumar Masarautar ta ce, za ta ci gaba da ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma zamananta da ayyukan noma.
Waɗannan tsare-tsare da ta ce sun haɗa da inganta ababen more rayuwa na noma, da inganta ɗorewar muhalli, da inganta samar da abinci, duk tare da kiyaye al’adun gargajiya da na musamman na yankin.
