Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ma’aikatar Al’adu, Fasahar Nishaɗi da Yawon Buɗe Ido ta Nijeriya ta nesanta kanta da wani labarin da aka buga a baya-bayan nan da ke nuna rashin jituwar diflomasiya tsakanin Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ma’aikatar ta ce, labarin da African Travel Times ta buga a ranar 12 ga Yuli, mai taken “A Bitter Irony: UAE’s Sanctions Undermine African Trust After Africa-Backed Win for UN Tourism Role,” ba ya nuna matsayin ma’aikatar ko Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.
Labarin ya nuna cewa goyon bayan da Nijeriya ta bayar na naɗin ‘yan Afrika a kwanan baya a Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido ta Majalisar ɗinkin Duniya ya dagula alaƙa da ƙasar UAE, musamman ma bayan da aka yi ta raɗe-raɗin hana ‘yan Nijeriya biza.
Sanarwar ta ce, “Ra’ayoyi da iƙirari da ke cikin labarin gaba ɗaya ba su dace ba. Nijeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa su na da kyakkyawar alaƙa ta cin moriyar juna, musamman wajen bunƙasa yawon buɗe ido da haɗin gwiwar al’adu.”
Ma’aikatar ta fayyace cewa babu wata sanarwa a hukumance daga UAE game da wasu sauye-sauyen da aka samu kan manufofinta na biza ga ‘yan Nijeriya.
A cewar ma’aikatar, sarrafa bizar ga ‘yan Nijeriya daga hukumomin UAE yana tafiya cikin tsari.”
Sannan ta yi kira ga mawallafa da su janye labarin, inda ta yi gargaɗin cewa irin wannan labarin na iya lalata dangantakar diflomasiyya.
“Muna raba kanmu daga abubuwan da ke cikin labarin kuma muna kira ga cibiyar da ta gyara labarin,” inji Barista Hannatu Musa Musawa, ministar fasaha, al’adu, yawon shaaatawa da kuma tattalin arziki.
Ta sake jaddada aniyar Nijeriya na ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin yawon buɗe ido na ƙasa da ƙasa da inganta harkokin diflomasiyya bisa amincewa da mutunta juna.
